Yusuf Abdullahi Yakasai" />

Limamin Mile 12 Legas Ya Bukaci Matasa Su Nisanci Halayen Banza

Babban Limamin Masallacin Juma’a na kasuwar mile 12 Lagos, Alhaji Buhari Yakubu, ya yi kira ga jama’ar Musulmi da mu sa tsoron Allah a zuciyarmu da rikon amana, wannan  shi ne mafita a garemu ba zagin shugabanni ba. Wannan kiran ya fito ne daga babban Limamin Masallacin mile 12, da ke Lagos.

Limamin  ya yi wannan jawabin ne a sa’ilin da yake ba da fatawar goron Sallah ga al’ummar Musulmi a hirar  da ya yi da wakilin LEADERSHIP AYAU JUMA’A.

Limamin ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a bisa kokarin da yake na tabbatar da karin zaman lafiya a Nijeriya. Alhaji Buhari Yakubu, ya roki ‘yan Nijeriya da su kauce wa nuna bambancin Addini ko kabila, yana mai cewa,  hadin kan kasa shi ne abin alfahari, ya kumu roki Musulmi da su kara damara wajen yin addu’a domin samun kara bunkasar tattalin arzikin kasa.

Da ya juya kan matasa,  Alhaji Buhari Yakubu, ya roki matasan da su zama masu biyayya ga iyaye da malaman Addini,  domin samun albarka da kuma samun ayyukan yi. Su kuma nisanci fadawa cikin munanan dabi’u na shaye-shaye, su kasance masu dogaro da Allah a duk yanda suka samu kansu.

A karshe, babban Limamin ya yi wa Nijeriya fatan alkhairi da dukkanin kasashen Musulmi na duniya baki-daya.

Exit mobile version