Connect with us

ADABI

Littafin ‘Rabi’atu’ Na Safiyya Mrs J Moon (19)

Published

on

Motsin shigowarta ya tashi Hindu wacce take barci, ta yamutsa fuska tana hararanta “Autan Ummi wai sai yaushe za ki yi hankali?” Zaunawa ta yi gefen gadon ta kamo hannun Hindu ta ce “Afuwan Maman twins Wallahi wani mutum na gani a parlornki yana da dan kyau kuma na ga ya yi kama da habibinki Mr Tsoho.” Duka Hindu takawo mata ta matsa tana dariya. “Baki da kirki Addawiyya yo yaron Alhji ne na biyu sunansa AbdulHameed, jiya ya dawo daga Egypt yin course, cikakken Doctor ne.”

“Oh ina mishi murna zamowar shi Doctor,  Allah ya sa ni ma wata rana na gan ni hakan bisa matakinsa.”

“Amin Autan Ummi.”

“Yawwa Aunty kin san abinda ya kawo ni gidan nan kuwa?”

“A’a sai kin fada.”

kasa ta yi da murya tace “Makiran matar can ta sato takardun kadarorin Alhaji ta saka miki a cikin sip, an jima zai zo nema in bai gani ba sai ta yi jagoran zuwa part dinki a yi bincike,  don haka yanzu zan dauka in mika shi zuwa part dinta,  ai in ta san wata ba ta san wata ba. Mugunta mu ma mun yi shi dan dai muna tsoron kwanciyar kabari ne.”  Cike da tarin mamaki Hindu ta ce “Autan Ummi samuwarki alkhairi ce a rayuwarmu, godiya nake yi miki mara adadi.”

“Kada ki damu aunty Allah yana tare da mai gaskiya.”

Ba tsoron komi Addawiyya  ta shiga parlorn Hajiya Karima,  ba kowa ciki don haka direct ta wuce bedroom dinta ta bude bedside drawer ta saka ta fito da sauri ta bace kamar walkiya. “Autan ummi me hakan ke nufi?” “So take Uncle tsoho ya sake ki ki bar mata gidan ta ci gaba da mulki don tace tunda kika zo komi ya lalace mata ta rasa gane kan mijinta.”

“Ikon Allah sai kallo, to ta Allah ba nata ba, zama daram a gidan nan.”

“Zancenki hakkun Aunty.” Da yammacin ranar suna kitchen girki suke yi. Hayaniyar Hajiya Karima ta yi musu sallama fadi take “Wallahi yau dubun barauniya ya cika,  dama don arzikinshi kika aure shi ‘yar matsiyata, to ki sani mu kam ba za mu lamunci sata ba a irin wannan gidan mai cike da nagarta.”

“Ki min shiru na ce Karima ko in saba mi ki, wai me ye kikeyi haka?” Alh. Muktar faban haka cikin kunar rai.

Tsaye su Addawiyya suka yi suna kallon ta. Alhaji yace “Hindu wasu takardu nake nema ban gani ba shi ne na ce ko kin gan su?”

“A’a Alhaji ban gan su ba sam.”

“K’arya take yi ita ta sace don haka dole abincika ko ina na cikin dakinta.”

Wani kallo Addawiyya ta doka mata tana girgiza kai tare da cije labba. “Ke uwarki kike wa wannan kallon?” Ta ce da Addawiyya cikin watso mata dakuwa. “A’a sai dai ina mawa Marka ce matar Basharu.” A fusace tayo kan Addawiyya Alhaji ya tare ta “Ke! Ban son sokarci a nan wurin,  ina ce tambayarta kika yi ta kuma ba ki amsa?” Cikin kuka Hajiya Karima ta ce “Su malam fa ta kira sunansu, suna can kwance cikin kabarinsu ta tashe su.” Kallon mamaki Alhaji ya saukewa Addawiyya domin sam bai kawo mahaifan Hajiya Karima ta ambata ba. Zai yi magana ta riga shi da cewa “A’a Alhaji ni kam ban san sunan iyayenta na kira ba, sunan zuwa min ya yi kawai a baki amma ni ban ma san wasu masu suna hakan ba.”

Jinjina kai Alhaji ya yi ya ce “To kin dai ji ba da su take yi ba don haka sai ki kama mana baki haka nan, kina bare shi kamar yarinya.”  Ga dariya amma ba halin yin shi. Tana hararan Addawiyya ta ce “To na ji,  amma sai an yi binciken nan an gano barawo yau.” “Karima fice ki ba ni wuri tun ban saba mi ki ba.” Hindu ta yi saurin cewa “A zo a yi binciken Alhaji ko za a gano mai halin beran.”

“Dear ba za a yi ba na ce, kaya dai nawa ne to ba komi kowa ya dauka nauyi ya rage min.” A fusace Hajiya Karima ta fada bedroom din Hindu tana masifa, “Ai Wallahi sai na duba haka kawai a cuce mu ina ji ina gani taf ba zai sabu ba kam.” Alhaji zai bi ta Hindu ta rike shi tana girgiza mishi kai,  a kan dole ya ja ya tsaya amma ranshi in ya yi dubu ya baci. Tsawon mintuna Sha Biyar Karima tana bincike amma ba ta ga komai ba hankalinta yayi mugun tashi.   Ayyanawa take cikin ranta ‘Anya kuwa Khairi ta kawo file dakin nan kuwa?’

“Malama ki fito mata a daki hakan nan tun kafin ranki ya baci.”

Jiki ba lakka ta fito, fuskanta ya jike da gumi sai sharcewa ta ke yi da hanunta, ta makure gefe tana zare idanu na rashin gaskiya.   Kallo daya Alhji yayi mata ya kau da kai yace “Allah ya shirya ki Karima, Allah ya sa ki bar kage a rayuwarki.” Da karfi Addawiyya ta amsa “Amin Abba.”

Ta ja jiki a sanyaye za ta bar parlor  Addawiyya ta ce “Abba a je a bincika part dinta ita ma mu gani ko yana can tunda dai ba a gani a inda take tsammani ba.”

“Ok je ki duba Rabi’a, kuma ki bincika da kyau.”

“An gama Abba. ”

Hajiya Karima ta soma masifa ita ta fi karfin sata don haka ba wanda zai yamutsa mata daki.   “Ai kam ba ki isa ba madam, yarda kika bincika na wata to ke ma sai an duba naki,  kuma ni da kaina zan jagoranta don haka ke yarinya zo mu je.” AbdulHameed yake fadin haka domin tun farkon dramar yana tsaye a bakin kofa yana kallo.

“Alhaji ka raba ni da danka tun kafin in dau mataki a kanshi.” Hajiya Karima ta ce cikin hargagi. Bai kula ta ba ya ce  “Abdul ku je ku duba, ke kuma Karima dawo ki zauna har su dawo,  za ta yi magana ya daka mata tsawa ba shiri ta dawo ta zube saman kujera tana hararan Hindu.

A cikin mintuna kadan suka dawo dauke da file suka mikawa Alhaji. Tuni Hajiya Karima ta soma rantsuwa tana hawaye,  wai baki suka hada suka kulla mata sharri. Kada kai kawai Alhaji Mukhtar ya yi tare da ficewa zuwa part dinsa ba tare da yace komi ba,  Abdul hameed ya mara mishi baya. Addawiyya ta dubi Hajiya Karima ta sheke da dariya ta ce “In za ka gina ramin mungunta to gina shi kadan don gudun wata rana zai iya zurmawa da kai ciki.”  Ta kara kwashewa da dariya.

“Da ni kike yin zancen yarinya,  za ki ga yadda zan mai da ke.”

“Uhm Hajjaju ma’abociyan sabon Allah, to ki rubuta ki ajiye ni Addawiyya ba dai mutum ba sai dai Allah,  kuma ki sani ni da kaina na kai miki file din dakinki kamar yadda kika turo fingilallaliyar ‘yarki ta kawo nan,  don haka ina ba ki shawara kada ki bari ki ci gaba shege ka fasa.”

Cike da fushi Hajiya Karima ta kawo mata mari ta ji an rike mata hannu gam koda ta juyo ta yi arba da Haydar yayi mugun hade rai, cikin kakkausar murya yace “Fice da arziki ko in ba ki mamaki.” Kafin ka ce me ta fice har tana tuntube,  saboda sosai take shakkan Haydar fiye da kowa a gidan hatta Alhajin kuwa. “Aunty please ki daina biyewa sokuwan matan nan kuna fada  kin ji?” “Insha Allahu zan kiyaye Haydar.”

“Madallah hakan shi ya fi.”  Ya juya ya fice bai ko duba inda Addawiyya take ba wacce a kollon daya da ta yi masa ta ji kirjinta ya harba da karfi,  a kasalance ta zame jiki ta shige daki tana mai jin wani yanayi na ziyartan ta wanda ta rasa gano ko me ye shi. Da dare suna cin abinci,  Addawiyya ta ce “Aunty matar can fa ta yi mugun tsorata da ni,  ba za ta kara marmarin kulla miki sharri ba.”

“Uhm Autan Ummi wallahi lamarin matar nan ya soma isa ta,  amma yanzu na yanke shawara na bar sake yi mata shiru balle ta zaci tsoronta nake ji.”

“Yawwa Aunty,  gara ki rika zare musu ita da ‘yarta ai.”

“Ke dai bari ai komi ya zo karshe,  za su sha mamaki na.”

“Weldon Auntyna amma dai ki dan dinga kauda kai.” Harara ta cilla mata suka sanya dariya a tare.

Washe gari Addawiyya na part din Hajja suna hiransu cikin nushadi,  Khairi ta shigo ba ko sallama,  ta dage ta dallawa Addawiyya mari, ko kafin ta sauke hannunta Addawiyya ta maida mata da martani kuma ba ta tsaya a daya ba a’a ci gaba ta yi da dalla mata zafafan maruka, AbdulHameed yana tsaye yana irgawa har sai da ta yi mata sau Goma Sha Biyu kwarara sanan ta dakata. Tuni Khairiyya ta zube tana tsala ihu,  fuskartata kuwa har ya kumbura. AbdulHameed ya soma dariya har da rike ciki, ya ce “bery good beauty, take my phone as a gift, ya tako ya fidda sim da memory card dinsa ya dora mata  phone din jiki, ta bi wayar da kallo ta ga iPhone ce ash calour, ta dago tana kallon shi ya sakar mata murmushi yana yi mata jinjina da hannu,  ya dora da cewa “Na jima ina son ganin wanda zai ci min uwar shegiyan yarinyan nan sai yau Allah ya kawo ki don haka tashi ma yanzu mu je shopping domin jin dadin abinda kika yi jiya da yau dole in karrama ki ainun.

“Gidanku nace Hameedu” Hajja ta ce da shi tare da yi masa dakuwa. “Amma kai kam an yi wofi mara raba fada sai zigawa.” Dariya ya saki tare da janyo hannun Addawiyya yace “Oyo come on beauty mu bar wa wannan old woman din matsuguninta ta yi fadarta ita daya.”

“kaniyarka na ce.” Yana dariya ya ja Addawiyya suka bar mata dakin.   Kamar doluwa Addawiyya ta biyo bayanshi,  suna shiga part din Hindu suka yi kicibis da Haydar. Wani faduwan gaba ya kawowa mata ziyaran bazata,  ta yi sauri dafe kirjinta cikin gwama numfashi,  “Wash!.” Ta furta a hankali.

“Kai dai ba ka jin magana ko?.” Yace da Handed.

“To me na yi kuma uban yan sa ido?”

“Hameed wallahi zan ci ma kaniya fa,  in ban da iskanci ka san kana da aiki a hospital amma ka zo gida ka rashe sannan kuma ka kashe wayarka don tsaban rainin wayau ka sa suna ta damu na da kira.” Sai da ya shafi sumar kansa cikin siririyar dariya ya amsa “To second Abba a yi min affuwa ba zan sake ba oga Ali gadanga kusar yaki.”

Dukan wasa ya kai masa kadan tare da ja mishi kunne,  sannan ya wuce yana murmushi. Ya juya zai bi shi ta yi hanzarin tura mishi phone dinsa a aljihun wandonsa ta baya ta ruga ciki da gudu. Dariya ya saki kadan ya furta “Zan zo miki da sabuwa dal an jima beauty.”

 

**

“Aunty yana da kyau sosai har ma ya fi Hameed kyau amma dai suna mugun kama da juna kamar ‘yan biyu.”

“Eh sosai suke kama da juna kuma Aliyu Haydar shi ne babba da Abdul Hameed.”

“Taf ai kam Hameed ya fi shi jikin girma sosai.”

“Ko autan ummi?”

“Eh Allah ya fi shi har da tsawo, shi dai haskene kadan zai nuna mishi.”

“To kodai ki na ciki ne? Oya zo ki  fada min wane ne gwanin ki cikinsu?” Dafe kanta ta yi kamar za ta yi kuka ta ce “Wayyo Aunty Hindu amma kin gama da ni wallahi.” Dariya Hindu ta saka tana shirin yin magana suka tsinkayi hayaniyar Hajiya Karima.

“Tofa ni Hindu na shiga uku!.’

“Kai Aunty kina ba da mata Wallahi yanzu kika gama cika baki.”

“Ina kike? gayyar tsiya mai siffan aljannu wallahi yau ko ni ko ku, zan ga uban da ya daure muku gindi a gidan nan da har za ki kusa sumar min da diya don kawai ta zo shashin kakarta.”

Kalllon tuhuma Hindu ta saukewa Addawiyya, ta yi saurin sauke kanta kasa tana motsa yatsun hannunta tana kuma dariya kasa-kasa.

 

Za mu cigaba gobe da yardar Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: