Connect with us

ADABI

Littafin ‘Rabi’atu’ Na Safiyya Mrs J Moon (20)

Published

on

Kunnenta ta kama ta matse da kyau “Oya fada min me kika yi wa ‘yar mutane?”  Kukan shagwaba ta saki har da hawaye, da sauri Hindu ta sakar mata kunne, tana cewa “Ayya sorry kanwata da zafi ko?.”

“Eh aunty.”

“To affuwan kin ji?.’

“Uhm! Uhm!! Ni ba ki min komi ba.”

Rungume ta tayi “Ina son ki Autan Ummi.”

“Ni ma ina son ki sosai Aunty uwa ta gari.”

“Ja’iran banza to waye ba ta gari ba?”

Cewar Hajiya Karima wacce takaicin shagwabar Addawiyya tuni ya gama cika ta ji take kamar ta rufe su da duka.

Juyowa Addawiyya ta yi ta sakarwa Hajiya Karima harara, a hasale ta yo kanta da bugu, Hindu ta tare ta da hanzari “Hajiya ya ishe ki abinda kike min a gidan nan, ki kama ragowar girmanki da ya rage, tun kafin ya karasa zubewa a idanuna tam.”

“Ba zan kama ba kin ji ko? ki yi duk abinda kike da niyya, gaiyar tsiya kawai, jinin hatsabibai, masu mugun abu, to Wallahi da ni kuke zancen, ku sani ni Karima na ci dubu sai ceto ballantana ku kananan kwari, na dauki aniyar ba zan bar kowa ya shakata ba a cikin ku sai na ba ku mamaki matuka, kuma dukan Khairi daidai ne da janyowa kanku jafa’i.” Tsaki Hindu ta ja “Allah shi ne gatanmu ba ki isa ki yi mana komai ba sai da izininsa kuma shi maji rokon bayinsa ne don haka mugun nufinki sai dai ya kare miki can amma mu kam mun rike babban takobin yaki da irinku wato addu’a.”

“Zaki gani yarinya ba dai kin ce mijina kike so ba hm!.’

“Na ga Alkhairi.”

Shiru hajiya ta yi don ba haka bokanta ya ce mata zai faru ba, a maimakon ta juya su kamar yadda yace sai ga shi ita ake yi wa hawan daba son rai. Hindu ta kalli Addawiyya cikin hade gira ta ce, “Autan Ummi me kika ma ‘yarta?”

“Mari na tayi ni kam na yi ta zabga mata har hawa 12, kuma ko yanzu ta kuma zuwa part din nan sai na yi mata hawa 24 wanda sai ta suma, in kuma kina ganin wasa nake yi ki turo ta ki sha kallo.’ Ta karasa tana yiwa Hajiya Karima kallon tabbatar da zancenta. Baki sake take kallon ‘yar karamar yarinya tana fada mata magana amma ta kasa cewa komai, domin zuwa yanzu lamarin yarinyar ya soma ba ta tsoro, shakkanta take ji sosai. ‘Anya diyar ga bata tare da iblisan junnu kuwa?’ Ta furta hakan cikin ranta.

“Ficemin a parlor ko in ba ki mamaki, wawiya kawai.” Maganar Hindu ya doki kunninta. “Ni ce wawiyar Hindatu?”

“Eh har da wofi ma ke ce, mara tunani kawai, wacce ba ta san kawaici ba.”

“Yes Wife kara mata da shashasha doluwa wanda girmanta bai mata amfanin komi ba sai mai da ta mashirmanciya da ya yi.” Alh. Muktar ne yake fadan haka sadda ya fito daga room dinshi da ke part din Hindu. Ko su Hindu ba su san yana ciki ba saboda ta baya ya shigo.

“Alhaji! ni kake watsawa kasa a idanu gaban wadannan banzayen?” Tasss!! Sautin fitar marin da Alh. Ya yi wa Hajiya Karima ke nan ya kuma nuna mata kofa ya ce “Gate out ko in miki abinda ya fi haka gabansu.” A fusace ta fice tana cewa “Haduwarmu da ku ba zai muku kyau ba har da kai munafukin mara adalci wanda dadin mace ya birkita mishi natsuwa.” Dariya Addawiyya ta yi da karfi duk don Hajiyan ta jiyo ta kuma ta jiyo tan yayin da kunyar tijararta ya kama Alh. Muktar.

“Dear bana ce da ke kada ki kuma kula ta ba?” Ya yi maganar ransa a bace.

“Affuwan Abban Hameed ka ga wacce ta tabo ta nan.” Ta nuna Addawiyya.

“Uhm Rabi’a me ya had’aki da ita?” Duk abinda ya faru ta fada mishi.

Ya ja numfashi ya ce “Good kin min daidai don Khairi ba ta da kunya sam, ta raina min uwa sosai amma zan dauki mataki a kai, shi kuma Hameed zan ci kaniyarshi maimakon ya raba sai ya kuma zigawa, kai halin Hameed sai shi a karshe ni da kaina na ba ki umurni duk sanda ta kuma gigin taba ki ki yi mata duka wanda ba za ta taba mancewa da ke ba, kin ji?”

“Tam Abba.” Ta amsa yana kallon gefen damarta tana murmushi.

“A’a Abban Hameed ba a haka kada ka zuga Autan Ummi ta yi aika-aika dan na san halinta komi za ta iya, abinda ya fi dai ka tara su ka yi musu nasiha tunda dukkansu yarinta yana damun su.”

“To zan duba yiwuwar hakan maman biyu.” Ya yi maganar cikin zolaya.

Kau da kai ta yi gyefe ta na murmushi.

Nan ya zauna ya kuma yi musu hasiha a kan amfanin hakuri da kau da kai.

“Beauty!! Beauty!!!” Ya shigo yana kwallawa Addawiyya kira, ita kam tana zaune a parlor tana buga game a laptop din Hindu. Zama ya yi gefenta tare da rufe laptop din “Ya kina ji ina kiran ki kika ki amsawa?” Sai da ta juya mishi manyan idanuta sannan ta amsa kamar mai ciwon hakori “Ban za ci ni ce ke da suna hakan ba.” Kallon ta yake yi ba ko kiftawa, ta mike ta shige bedroom ta bar mishi wurin. Tsaki ya ja mai sauti ya ture laptop din gefe ya mike ya fice bayan ya ajiye mata kwalin sabuwar wayar da ya sayo mata zai ba ta amma ta wani tsaya yi mishi yanga. ‘Wai ni ne yarinyar nan za ta yiwa yanga? lallai kuwa zan fita harkanta don kada ta ga kamar ina son ta ne’ wani tsakin ya kuma ja, ya furta “Ko cika budurwa ba ta gama yi ba amma ta san kan iskarancin iyayin mata.”

Haydar ya dube shi ya tabe baki ya mike ya shige bedroom dinshi, da harara Hameed ya bi bayanshi yana jin kamar ya bi shi ya rufe shi da duka na halin ko’inkula da yake nunawa mutum in dai ba lamarinsa ba ne to ba ruwanshi ko me za ka yi ba zai tambaye ka ba sai in dai kai ne ka gaji ka sanar da shi to zai saurare ka shi ma ba wani abin arzikin da zai tabuka ba sai dai kalmar yi sorry, kalmar da take mugun batawa Hameed rai ke nan duk sadda ya fada mishi ita.

Ranar Sunday da yammaci Addawiyya ta shirya za ta koma gida, Hindu ta rako ta har bakin mota tana jadda mata za ta yi kewarta sosai. “Aunty kada ki damu ina tare da ke ai, komi ya shige miki duhu ki kira ni a wayar Ummi zan warware miki.’

” Ok Allah bar kauna.’

“Amin.”

Sai da ta gyara zama a cikin motar sannan ta mikowa Hindu ledar da Hameed ya ajiye mata jiya wacce yake dauke da sabuwar waya ta kece raini.

“Ki ba shi kayarshi, ki ce ma sa Abbiena zai saya min in lokaci ya yi, kuma in na bata mishi rai yayi hakuri.” Amsa Hindu ta yi ba tare da tace kala ba dan ta san kila mutanenta ne suka hana ta amsa shi ya sa ba ta ja zancen ba. Suna dagawa juna hannu har ta fice gate.

“Aunty me ke damun sistern ki?”

“Babu komi Handed.”

“To me na yi mata da ta kasa amsan kyautana? Ko dai ta yi mata karama ce sai na canja mata wanda ta fi ta komai?”

“A’a babu ko daya Hameed, ina ga dai sabida Abbie yace sai ta soma unibersity za ta soma rike phone shi ne ya sa ta ki amsa.”

“Uhmm tam zan ko ajiye mata har sai ta soma jami’ar.” Dariya Hindu ta saki ta ce “A zubo maka abincin ne?” Ta kau da zancen. “No am ok, yanzu na ci snacks a wurin Ya Haydar.”

“Ok bari a bar shi ka ci an jima.”

“Eh, zan ci insha Allah.” Gyara zama yayi ya koma serious yace “Aunty ina son in yi aure, wacce yarinya kika ga ya dace ta zamo abokiyar rayuwata?”

“To fa!! Hameed ni kam ban san zabin da ranka ke so ba.”

“Aunty bana da zabi sai wanda kika zaba min domin mai yanayin rayuwarki nake so wacce ba ta da hayaniya ga iya tattali da tarin natsuwa, ko da kuwa cikin kannenki ne ina muradi.”

Shiru Hindu ta yi tana nazari zuwa can ta ce “Bana da kanne sai Addawiyya, ita kuma a kwai dan abokin Abbie da yake son ta.” Domin sosai Hindu take son Ubayyu ya auri Addawiyya. Yamutsa fuska Hameed yayi kamar mace yace “A’a ni ma bana ra’ayinta, ki dai nemo min wata koda cikin students dinki ne amma mai aji da kyau kuma mature enough nake so ba yarinya karama irin kanwarki Addawiyya take ko wa ma?” Dariya ta yi sosai. “To AbdulHameed zan duba na gani, amma hakika ka hada ni da aiki.” Dariya ya saka tare da mikewa yana cewa “Kawo sakon da zan kaiwa su Abbie don yau zan je na gan su duk da ba su san ni ba.”

“Ai ko suna ganin ka za su gane daga inda ka zo, saboda kamannin Abbanka da za su gani a tare da kai.”

“Aunty hoo, Ya Haydar shi ne ziryan Abba amma ni Hajja na biyo.”

“Haka dai ka ce amma sosai kuke kama da juna ku duka hudun.”

Ya shafi sajansa cikin murmushi “To na yarda Aunty, saura ki haifo mana brothers nd sisters masu kama da ke, kin ga an surka ke nan.”

“Uhm.” ta ce tare da mikewa ta nufi room dinta sai da ta kusa shiga ta juyo “A gaishe min da su Abbie sosai, a cewa Ummie ta yi min dambun zogale ka zo min da shi, ta kuma zuba man shanu ne ba man gyada ba.”

“Ok don’t worry I’ll tell her.”

“Thanks sai ka dawo, ka sayo min yalo farare tas nake so.”

“An gama our special mummy.”

Nuna shi ta yi da yatsa tana murmushi ta shige ciki.

“That’s why i lub u too much aunty, kina da kirki ga hankali da natsuwa, Abba yayi dacen mata yanzu kam, Allah ya ji kan Umma da rahama ya ba ta aljanna madaukakiya.”

“Amin ya rabbi brother.” Haydar ya amsa mishi. Juyowa yayi ya rungume dan uwan nashi sai kuma ya saki kuka mara sauti. Sabida tunowa da mahaifiyarsu da ya yi. Bubbuga bayanshi Haydar yake yi a sannu kuma yana yi mishi magana kasa-kasa da alama hakuri yake ba shi.

 

Za mu cigaba Talata da yardar Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: