Connect with us

KANNYWOOD

Littafin ‘Rubutun Fim’: Marubuci Babinlata Ya Sake Kafa Tarihi A Kannywood

Published

on

A karo na farko an kaddamar da littafin Hausa a yanar gizo. Littafin mai suna ‘Rubutun Fim’ shahararren marubucin Hausan nan da ya ga jiya kuma a ke damawa da shi a yau, sannan kwararren mai bayar da umarni a masana’antar shirin fim ta Kannywood, wato Bala Anas Babinlata, ne ya rubuta kuma ya wallafa.

Idan za a iya tunawa, Babinlata ne ya fara kirkirar kasuwar shirin fim ta Kannywood ta hanyar buga kwalin fim dinsa mai suna Tsuntsu Mai Wayo a shekara ta 1995, inda daga nan ne a ka samu dabarar cigaba da buga kwalin fim a na sayar wa ’yan kasuwa, su kuma su na sayar wa daidaikun mutane.

A yanzu kuma marubucin kuma darakta finafinai ya kirkiri sabuwar dabarar yin kasuwancin littafi a kasuwar Adabin Kano, littafin da ya kunshi koyar da dabarun yadda a ke rubuta fim. Kaddamar da cinikayyar fim din a shafin Facebook, shi ne irinsa na farko a tarihin masana’antar Kannywood da Kasuwar Adabin Kano.

Shi dai littafin mai suna ‘Rubutun Fim’ wani babban kundi ne da marubucin ya samar, domin ya yi wa kananun marubuta masu tasowa jagora ta fuskar rubuce-rubucensu, yadda za su inganta rubutunsu ya barranta daga baragada da harigido har ya zamo abin yabo da yabawa. Kuma littafin ya na rarrabewa tsakanin labari da tsarawa da kuma rubutun fim da na zube da kuma gama-garin zantuka da labarai.

An yi bikin kaddamarwar da littafin ne ranar Litinin da ta gabata, wacce ta yi daidai da 8 ga Yuni, 2020, a farfajiyar marubucin da ke kafar sadarwa ta zamani wato facebook mai suna Bala Anas Babinlata da misalin karfe 11:00 na safe zuwa karfe 1:00 na rana, inda fasihin furodusa a Kannywood, Malam Ahmad Alkanawy, ya zamo mai gabatar da taro.

Duk da kasancewar taron kaddamarwar ya zo da wani sabon salo wanda ba a saba da shi ba ko ma a ce marubutan Hausa ba su taba yin sa ba, wato taro a yanar gizo maimaikon fuska-da-fuska, amma hakan bai hana taron yin armashi da halartar manyan baki da marubuta da malaman adabi da kuma ‘yan jarida ba.

Daga cikin manyan bakin da su ka halarci wannan taro akwai Shugaban Taron kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar NOUN Farfesa Abdalla Uba Adamu da tsohon shugaban kungiyar marubuta ta kasa reshen jahar Kano (ANA Kano) Farfesa Yusuf Adamu da takwaransa shi ma tsohon shugaban kungiyar Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), Farfesa Ibrahim Malumfashi shugaban sashin nazarin harsunan Najeriya na jami’ar Jihar Kaduna da Farfesa Adamu Tanko.

Kuma akwai Dr. Ahmad Sarari, shugaban hadaddiyar kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta kasa, fitaccen mawaki kuma Dan Amanar Bichi kuma Sarkin Wakar Sarkin Dutse Alhaji Aminu Ladan Abubakar (ALA). Haka nan akwai Editan LEADERSHIP A YAU kuma fitaccen marubucin finafinan Hausa Nasir S. Gwangwazo.

A gefe guda kuma ga Hajiya Rahma AbdulMajid, shugabar kungiyar marubuta mata zalla ta ‘Mace Mutum Writers Association’, sannan akwai marubuta irin su Fauziyya D Sulaiman: Hajiya Hadiza Nuhu Gudaji, Al-Hussain Burji, Rahma Sarki Aliyu, Maimuna Idris Sani Beli, Kabiru Yusuf Fagge, Shafi’u Dauda Giwa, Ahmad Abubakar Amaryawa da dai sauransu.

Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kani kuma Babban Mai Gabatar da Taro, Isma’il Na’abba Afakallahu, ya bayyana cewa, hukumar ta sayi kwafin littafin a kan Naira 50,000. Sannan sauran manyan baki da su ka soma seyen nasu kwafin akwai Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda ya sayi kwafi Biyar a kan Naira 5,000, Farfesa Adamu Tanko shi ma ya sayi kwafi biyar a kan Naira 5,000.

A gefe guda kuma Aminu Ladan Abubakar (ALA) da ya sayi littafin kwafi 10 a kan Naira 10,000, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON shi ma ya sayi littafin kwafi 10 a kan kudi Naira 10,000, Hajiya Rahma AbdulMajid ita ma haka. Ita kuwa marubuciya Fauziyya D. Sulaiman, shugabar gidauniyar nan ta tallafa wa marayu da marasa lafiya da kuma masu bukata ta musamman (CHNF) ta sayi kwafi 10 a kan kudi Naira 10,000, don a raba wa kananan marubuta masu tasowa, sannan ta sayi nata kwafi biyu a kan Naira 5,000. Hajiya Rahma Sarki Aliyu ta sayi kwafi uku a kan Naira 10,000.

Kamfanin AGF Multimedia ya sayi kwafi biyar kan Naira 5,000, Anka Motion Pictures ya sayi kwafi 20 a kan Naira 20,000, kungiyar MOPPAN ta sayi kwafi 20 kan kudi Naira 20,000, Kannywood Entertainment ya sayi kwafi 10 kan Naira 10,000, Al-Hussain Burji ya sayi kwafin littafin ne a kan kudi Naira 100,000, Hajiya Fati Niger kuwa ta sayi kwafi 10 a kan Naira 50,000. Nasir Gwangwazo ya sayi kwafi daya a kan Naira 5,000.

Haka dai a ka yi ta siyan wannan littafin, saboda muhimmancin sa da tarin alfaninsa. Don haka a ce wannan taro kwalliya ta biya kudin sabulu.

Marubucin littafin, Sir. Bala Anas Babinlata, a cikin jawabinsa ya bayyana dalilinsa na wallafa wannan littafi kamar haka:

“Dalilina na yin wannan littafin biyu ne; na farko Ina so na bayar da gudunmawa ta ga ‘yan uwana marubuta da masu sha’awar son yin rubutu musamman na fim. Na biyu wanda shi ne kashin bayan wallafa littafin dan yi bayaninsa a takaice duk da dogon labari ne. Da fatan za ku jure karantawa.

“Rubutu shi ne kashin bayan kowane fim. Wannan ne ya sa fina-finan da a ka yi a baya su ka yi tasiri, saboda akwai hannayen marubuta, musamman na littafi a ciki. Idan mutum ya na da ja ya dubi gidan talabijin na Arewa24 kusan duk marubutan dirama dinsu ‘ya’yanmu ne marubutan littafi. Sanin muhimmanci marubuta a harkar fim ya sa na rika janyo marubuta ta hanyar ‘workshops’, don su bayar da gudunmawarsu. Rubutattun Littattafai su na taimaka wa sosai a duniya wajen samar da labaran fim, amma mutuwar kasuwar littafi ko na ce sauyawar kasuwar daga ‘bookshop’ zuwa ‘online’ ya kassara samuwar nagartattun littattafai.

“A karshen shekarar da ta gabata (2019) na gano kasuwar littattafan ba mutuwa ta yi ba, makaranta sun rasa in da za su samu littattafan su saya ne, wala a ‘bookshop’ ko ‘online’. Na gano wannan ne daga tattaunawa da mutane a Facebook. Wannan ne dalilin da ya sa na kafa ‘group’ a Telegram, inda marubuta za su gana da makaranta, su kuma nemi duk littafin da su ke so su saya ta ‘book on demand’. Sai dai in da gizo ke sakar, lokacin da mu ka kira taron marubuta, an samu halarta, amma sai mu ka fahimci yawancin marubutan na da can da na Yyanzu sun samu tabuwar tattalin arziki ta yadda ko tsofaffin littattafansu ba za su iya bugawa a kwamfuta ba; ba wai maganar dab’i ba. Wannan sai ya sa mu ka sake tara marubutan a ofis din Farfesa Yusuf Adamu da tunanin mu hada kudi mu yi kamfanin ‘book on demand’ da ‘website’. A nan Farfesa Adamu ya janyo hankalina da kada a yi ta surutun na kawo marubuta ofishinsa a na yi mu su wayo. Duk da mun yi dariya, amma maganar ta tsaya min a rai sosai.

“Sai na shiga tunanin ta wacce hanya zan bi na taimaka a kafa wannan kamfani tun da marubuta na cikin wani yanayi? A wannan gabar ne na karkade wannan littafin nawa ‘Rubutun Fim’ na kammala shi da tunanin idan mu ka tara masoyanmu mu ka gabatar da shi, dan abinda a ka samu sai na yi amfani da su na kafa ‘Hausa Nobels Foundation’ da za ta samar da ‘website’ da ofishin yin ‘book on demand’ da zai amfani duk marubuta.”

An fara taro lafiya kuma har a ka kammala lafiya kalau.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: