Littafin ‘SAI YANZU’ Na Hanne Ado Abdullahi (8)  

Sai Yanzu

Baffa ya samu ya shiga FGC dake kano. Da farkon Abbansa ya so ya sa shi ta kwana saboda yana so ya mai da hankalinsa kan karatunsa amma shi yaron da kansa ya ki. Ba kuwa wani abu ba ne ya hana shi tun da in don karatun islamiyya ne yayi sauka gab da tafiyar sa secondary. Saboda karatun nasa hawa biyu ne. Ya yi a makaranta. Idan ya dawo gida Abbansa ya dora masa. Sai karatun makaranta ya zamar masa mai mai. Dalilinsa na kin zuwa makarantar kwana yawan kudin da ya ga an rubuta za a kashe. Ya san kuwa idan ya gaya wa Abbansa sai ya ganganda ya nemo su. Duk da yaro ne shi, amma yana da zurfin tunani. Haka zalika ya san halin da suke cike. Sai yayi wa Abban nasa karya da cewar ta jeka ka dawo aka dauke shi. Shi ma kuwa sai da aka ji jiki aka samu aka hada kudin litaffi da na uniform da kuma kudin makaranta.

 

Cike da sa’a kuwa ya fara zuwa makarantar. Kullum da kafa yake takawa tun daga unguwa uku wajen masallacin Faruku har FGC Kano. Ko Abban ya ba shi kudin bus sai ya ki karba. Kuma tun karin safe da zai yi a gida ba zai sake cin komai ba har sai ya dawo gida, saboda kawai ba ya son Abbansa ya wahala. Ga wadannan ‘yan lukutayen na Gwaggo kamar yadda yake kiran su Zahra da Humaira. Da an saya musu kaya kwana kadan sun cika su. Kamar ana hura su. Ga Gwaggon ta bata su. Indomie pakitin guda idan an dafa tsaf za su tashi da ita. Haka idan awara ce suka samu yanka hudu manya, ita ma sai dai labari. Abban su kuwa da ya lura suna son indomie ko za a zauna ba ci abinci a gidan ba sai ya sayo musu ita.

 

Haka ya dada sanya Baffa daurewa wasu abubuwa na rayuwa. Shi bai cika surutu ba, gwanda ma da Gwaggonsa tun da ita mace ce mai harka. A makarantar ma da yake zuwa kafin term biyu malamai sun fara sanin sa saboda kwazonsa. Term din farko ne kawai da yaje a makare ya yi na biyar. Ana biyu kuwa ya dauko kambunsa  na daya. Yana term na uku ya dawo gida ya tarar da Gwaggonsa ba ta da lafiya. Amma ya rasa gane dalilin da Abbansa yake ta murna da ciwon nata. Sai da aka dauki watanni sannan ya gane ashe cike ne Gwaggonsa take da shi. Gwaggonsa na tashe da tsohon cikinta lokacin haihuwa ko yau ko gobe, Allah ya jarabci Humaira da Zarah da cutar kyanda.

 

Hankalin Gwaggo ba karamin tashi ya yi ba. Ga matsin rayuwa da ake ciki. A kan yaran nan ta salwanta da duk wata kadara da take da ita. Sun kwashe sama da sati uku a asibitin Hasiya Bayero. Dan kiwonta da dan kayan dakinta duk haka ta tattara su ta sayar a karye saboda ta samu na sayen magani. A wannan lokaci duk gidan sai da su ka jigata. Mallam Jibo kullum yana zarya daga gidansa nan unguwa uku zuwa gidan sarki. Ga sana’a ta kullum fita ake a nemo abin da za a ci. To, ba shi da natsuwar da zai ma zauna ya yi sana’ar tasa. Ita kanta uwar yaran ga halin da take ciki. Ciwon nan kuwa da ya kama su Humaira sai da aka fid da rai da su.

Mallam Jibo sai kuka yake ya na fadin “Allah kar ka dauki ahalin Mallam Musa a hannuna.”

 

Ganin halin da suke ciki ya sanya shi garzayawa gidan Honourable domin ya sanar da shi. Shi ba kudin magani yake nema ba, amma dai wani shakikinsu ya san halin da suke ciki. Baima samu ganinsa ba sai, Mommy ya samu. Yana gama gaya mata halin da suke ciki ta rufe shi da fada. Fadi take “in ban da rubar tsiya meye na kai su asibiti. Abin da man kifi a ake bayarwa da kuma bommi, amma shi ne kai saboda ka san akwai mai kudin banza ka dauko tsawo kamar bishiyar turare ka taho a ba ka kudin magani. Sai ka san nayi baitulmalin naka ba ya nan”. A haka cike da bakin cikin abin da ta gaya masa, ya bar gidan. Asibitin ya dosa saboda ya san ya bar su tsakanin rayuwa da mutuwa.

 

Shi bai taba sanin kyanda idan ta yi mugun kamu har dayewa jikin yara yake ba kamar sun kone sai a kan su Humaira. Shugabar asibitin ya samu a tare da su watau DR Binta Jibir tana duba su, take ta canza masu wasu alluran. Yaje wajen biya aka yanka masa makudan kudi. Ya dawo yake sanar da Wabili. Tace “Mallam yi sauri gida akwai ragowar rago guda daya da aka barshi domin hakika a sayar da shi kawai”.

“Gaskiyar ki Wabili. Ga na gaban mu yaushe za a tsaya yi wa wanda bai zo duniya ba. Bari in yi sauri in je gidan. Bai fi awa daya da tafiya ba, ya dawo da kudi ya karyar da ragon. CMD Binta Jibir tana gefe taji ya na yiwa pharmacist din bayani ya taimaka ya karbi kudin da yake da su, shi kuma ya yi alkawarin ko zai kwana  ya wuni yana sana’arsa zai hado masa sauran kudinsa. Shi dai bukatarsa ya ba shi alluran complete a fara yi wa yaran.

“Mallam sana’ar me kakeyi” CMDn ta tambaye shi. “Likita wanki da guga nake yi a unguwarmu”. Ya amsa mata cikin ladabi.

 

Ta mai da hankalinta wajen pharmacist din. Sannan tace “gibe him all the drugs as well as the injection and send me the bill”. Sannan ta juya wajen Mallam Musa tace “ka yi hakuri zai ba ka magungunan. Allah ya ba su lafiya”.

“Amin amin likita na gode”, ya fada yana mai rissinawa. Kafin ma ya ci gaba da godiyar  ta yi gaba abinta ta barshi a nan. Ya juya wajen pharmacist din yana kokarin mika masa kudin da ke wajensa. “Barshi Mallan ai Dr ta biya duka”  Sujudu shukur ya tsugunna yayi saboda murna. Cikin hukunci Allah ana fara amfani da sabbin magungunan nan sauki ya dinga samuwa. Kafin kwana hudu kamar ba su ba. Har sun fara karbar abinci. Kafin sati har ramarsu ta fara tafiya. Sai bayan sati biyu da faruwar haka sannan aka sallame su. Har ofis din CMD suka je suka yi mata godiyar alkhairin da ta yi musu.

 

Baffa ya na form two second term, Allah ya sauke Gwaggonsa lafiya ta samu ‘ya mace. Tun da aka wanke yarinya aka mika masa ya rike ta tam a hannunsa ya kasa dauke idonsa daga kanta. Wata makociyar su ce data shigo barka tace “Baffa ka kama yarinya ka rike gam ka hana kowa”  Duk dakin aka sa dariya. Shi dai murmushi yayi. Ya juya ya kali Gwaggonsa, ya ce “Gwaggo tana da kyau. Ta fi kowa kyau a gidan nan. ki ba ni ita”.

“Ai dama taka ce Baffa”.

Tun daga lokaci kuwa ya dauki aniyar ba ta kulawa. Ranar suna ma shi ya zaba mata suna, inda ya sa Abbansa ya rada mata Hamida. Yarinyar nan haka aka yi sunanta ba tare da hakika ba, saboda kudin rago ya tafi a hidimar asibitin su Humaira.

 

Ranar suna Baffa ya na ta jira ya ga an yanka rago ya ga shiru. “Abba sai yaushe za a yanka ragon suna”? Ya tambayi Abbansu. Sai da ya shafa kansa, sannan ya ce “Baffa yankan suna sai mutum yana da halin yinsa yake yi. Idan babu ba wajibi ba ne”. “Ke nan ita Hamida ba za a yanka mata ragon suna ba?” “Ka yi hakuri Baffa ko a gaba na samu dama sai in yanka mata. Ai na so ma ko da dan akuya aka samu a yanka to bai samu ba ne” Shiru ya yi bai ba shi amsa ba. Tun daga wannan lokaci Baffa ya koma wajen Sale mai Shayin a nan unguwarsu. Ya dinga yi masa wanke wanken kofunan da farantan indomie da aka yi amfani da su, shi kuma ya na bashi lada. Ga shi ya yi sa’a sun samu hutun makaranta. Kafin wata kuwa sai da ya hada kudin dan akuya. Bai yi shawara da kowa ba sai ganinsa kawai aka yi ya shigo da shi wai ga shi ya kawo a yi wa kanwarsa Hakika da shi. Da kyar aka lallaba shi ya yarda a bar mata a kiwata mata shi tunda hakikar ba wajibi ba ce.

 

Baffa bai taba nuna shaukinsa a kan yara ba, sai a kan Hamida. Idan Zahra da Humaira za su kwana suna kuka ba zai kula da su ba. amma ita ko yaya ya ji kukanta yanzu zai bar abin da yake ya dauke ta. Kafin wata biyar kuwa ya koya mata dan lasar abubuwa, saboda komai ya samu na ci sai ya lasa mata. Balle ma da yake tana da wata shida Wabilin ta sake samun ciki inda ta haifi namiji. Tun yana tsumma Mallam Jibo yayi masa huduba da Musa. Shi ma suna kiransa da Walid. Zuwansa bai dakushe tauraruwar Hamida ba. Shi dai Baffa Hamida ce tasa. Wani lokaci har korafi Wabili take yi na halin ko in kula da yake nunawa a kan ‘yan biyunta. Ranar nan ya gaji yace mata wai sun cika kumatu ba su da kyau. Ita kuwa Hamida ta fi su kyau. Dariya ta yi tace “A ga dai mai kyan a cikinsu. Amma kowa ya kalli su Humaira ai ya san kyawawa ne. kai dai kawai son kai za ka yi.” Murmushinsa na sabo yayi. Ko fita zai yi daga gidan sai yayi mata wayo, in ba haka ba ya tafi ya bar Wabili da aikin rarrashi. Komai kukan da take da ta ji muryarsa za ta yi shiru.

Exit mobile version