Connect with us

WASANNI

Liverpool Ba Za Su Iya Lashe Kofin Firimiya Ba Duk Da Sun Ci Wasa Biyar A Jere

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jamie Carragha ya bayyana cewa tsohuwar kungiyar tasa bazata iya lashe kofin firimiya ba saboda batada karfin ragowar manyan kungiyoyin da suke buga gasar.

Carragha ya fadi hakane bayan da kungiyar ta Liverpool ta buga wasa tasamu nasara daci 2-0 da kungiyar Tottenham a filin wasa na Wembley a ranar Asabar din data gabata.

Ya kara da cewa duk da cewa kungiyar ta magance matsalolin da yakamata ace tayi maganinsu  a lokacin da ake siye da siyarwar yan wasan a watannin da suka wuce ta hanyar siyan Mai tsaron raga Allison Becker daga Roma da Nerby Keita.

Yaci gaba da cewa kungiyar tanada matsala a yan wasan baya domin ana yawan saka musu kwallo a raga wanda hakan ba karamar matsala bace amma kungiyar batayi maganin hakan ba.

Yace dole sai kungiyar tayi maganin matsalolinta idan har tana son ta iya lashe kofin na firimiya na wannan shekarar duk da cewa kungiyar ce a matsayi na daya akan teburin Firimiya bayan buga wasa biyar.

A cewar Carragher, idan har suna son su shiga sahun manyan kungiyoyi to dole sai suna lashe kananan wasanni da a baya kungiyar  bata iya samun nasara akansu.

Liverpool din dai zata buga wasanta nagaba da abokiyar hamayyar ta wato Everton a filin wasa na Anfield a sati mai zuwa.

 
Advertisement

labarai