Liverpool Ta Kammala Sayan Ibrahima Konate Daga RB Leipzig

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta amince da biyan kudi domin zayan dan wasa Ibrahima Konate, dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig, bayan da ba za ta mallaki Ozan Kabak ba.

Konate, mai shekara 22, yana cikin tawagar Faransa ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 da za su fara gasar Turai ranar 31 ga watan Mayu kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan baya da suka haska a kakar bana a kasar jamus.

Rahotanni na cewar mai tsaron bayan yana da kunshin kwantiragin fam miliyan 34 ga duk kungiyar dake son daukarsa, idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba wanda hakan yasa kungiyoyi da dama sukayi zawarcinsa.

Liverpool tana da damar kin mallakar Kabak wanda ke buga mata wasan aro daga kungiyar kwallon kafa ta Schalke 04, inda ta sanar da dan wasan hakan, shi kuma ya fara tattaunawa da wasu kungiyoyin.

Cikin yarjejeniyar da Liverpool ta shiga wajen dauko Kabak zuwa filin wasa na Anfield a watan Janairu har da batun mallakar dan kwallon kan fam miliyan 18 idan ya taka rawar gani a kungiyar.

Kabak ya buga wa Liverpool wasanni 13 daga baya aka ajiye shi, tun bayan 1-1 da kungiyar ta tashi da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ranar 24 ga watan Afirilun da ya gabata.

Konate ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig wasanni  21 a kakar wasan bana, bayan da kungiyar ta karkare kakar Bundesliga a mataki na biyu, za ta wakilci Jamus a Champions League a badi.

Ranar Lahadi itama kungiyar kwallon kafar ta Liverpool ta samu gurbin wakiltar kasar Ingila a Champions League a badi, bayan da ta doke Crystal Palace a gasar Premier League ta yi ta uku a teburi.

Exit mobile version