Abba Ibrahim Wada" />

Liverpool Ta Yi Wa Mane Farashin Fam Miliyan 200

Sadio Mane of Liverpool during the Premier League match at Craven Cottage Stadium, London. Picture date: 17th March 2019. Picture credit should read: Craig Mercer/Sportimage via PA Images

Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool tayiwa dan wasanta, Sadio Mane, farashin kudi fam miliyan 200 ga duk kungiyar da take son siyan sa a kakar wasa mai zuwa bayan da kungiyar Real Madrid ta bayyana sha’awarta ta siyan dan wasan.
Dan wasan dai yana daya daga cikin ‘yan wasan da tauraruwarsu take haskawa a kungiyar ta Liberpool inda kawo yanzu yanada kwallaye 17 a kungiyar kuma kwallaye 13 dayaci duk a wasanni 17 na kwana kwanan nan yaci su.
A kakar wasan data gabata dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nemi dan wasan mai shekara 26 a duniya a lokacin Zidane yana kungiyar sai dai daga baya bayan Zidane din ya ajiye aikin koyar da Real Madrid din sai kungiyar ta dakatar da nemansa.
Tun bayan da mai koyarwar yadawo kungiyar aka fara rade radin cewa zai sake neman dan wasan dan asalin kasar Senegal inda kuma tuni ya bayyana wa shugaban kungiyar cewa yana son idan da hali a siyo masa Sadio Mane.
Hakanne yasa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sanya farashin kudi fam miliyan 200 wanda shine farashin da PSG ta biya wajen Siyan Neymar a shekara ta 2016 kuma hakan zaisa Real Madrid ta hakura da neman dan wasan.
Shugaban gudanarwar Real Madrid, Florentino Perez dai a shirye yake domin siyan duk dan wasan da Zidane yace yana bukata domin fara gogawa kafada da kafada da abokiyar hamayyarsu Barcelona wadda itace ta daya a laliga.
Real Madrid dai tayiwa Liberpool alkawarin cewa zata shigar da daya daga cikin ‘yan wasanta da suka hada da Gareth Bale da Marco Asensio da ko James Rodriguez domin Liberpool din taji dadin siyar da Mane.

Exit mobile version