Dan wasan gaba na Liverpool, Sadio Mane yace kungiyarsa ta Liverpool za ta iya doke kowacce kungiya a kasar ingila har ma da kungiyoyin nahiyar turai.
Mane, wanda a yanzu haka aka dakatar dashi wasanni uku bayan da aka bashi jan kati a wasan da Manchester city ta dokesu daci 5-0 ya ce, suna da ‘yan wasan da zasu iya doke kowacce kungiya.
Ya ce, suna da karfin tawagar yan wasa, suna da magoya baya masu taimakawa yan wasa ta hanyar karfafa guiwa sannan kuma sunada babban koci
Ya kara da cewa kowanne dan wasa a kulob din a shirye yake da ya bayar da kowacce irin gudummawa don ganin sun samu nasarar cin kofi a wannan kakar da aka fara.
A jiya ne ne dai Libverpool din ta lallasa kulob din Leceister city daci 3-2 har gida a wasan firimiya da suka fafata a wasan sati na 6