Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kociyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp yanason sake neman dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ousmane Dembele.
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dai bata bukatar dan wasa irin Dembele sakamakon ‘yan wasanta na gaba duk suna da lafiya sai dai yanayin yadda dangantakar dan wasan take tafiya a kungiyar yasa ake ganin dan wasan zai iya barin kungiyar.
Rahotanni dai sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta iya biyar Liberpool kudi kusan fam miliyan 85 idan har kungiyar tasa ta amince za ta rabu da dan wasan dan asalin kasar Faransa.
Dembele dai yana cikin kakar wasa ta biyu a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona sai dai kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa dan wasan baya zuwa filin daukar horo akan lokaci hakan yasa kungiyar tafara ajiyeshi a wasa.
Barcelona dai bata da niyyar siyar da dan wasan nata sakamakon saura shekara uku da rabi kwantaragin dan wasan ya kare amma kuma idan har aka taya dan wasan da tsada za ta iya rabuwa dashi.
Dan wasan dai an fara buga wasa dashi acikin ‘yan wasan farko sau 19 tun bayan daya koma kungiyar a kakar wasan data gabata sannan kuma ya wakilci kasar Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya.