Connect with us

WASANNI

Liverpool Za Ta Sayi Koulbaly Daga Napoli

Published

on

kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta mika bukatar sayen mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta  Napoli, Kalidou Koulbaly, dan wasan dake matsayin mai tsaron baya da kungiyoyin Turai ke rububi a yanzu saboda kwarewarsa.

Baya ga Liverpool din kungiyoyin Firimiya ciki har da Chelsea da Man United na sahun gaba da suka nuna bukatar sayen Koulbaly dan Senegal mai shekaru 29, ko da dai Liverpool din ce ta fara tuntubar dan wasan a hukumance.
Matukar dai Liverpool ta yi nasarar sayen dan wasan kenan kungiyar zata hada zaratan masu tsaron baya da ake kallonsu a matsayin mafiya karfi da rashin tsoro wato Kalidou da birgil ban Dijk dai dai lokacin da kungiyar ke shirin lashe kofin firimiya karo na farko cikin shekaru 30.
Koulibaly wanda Napoli ta sanyawa farashin yuro miliyan 90 masu sharhi kan al’amuran wasanni na ganin abu ne mai wuya Liverpool ta iya sayen dan wasan a wannan farashi musamman ganin yadda coronabirus ta kassara bangaren kudaden shigar kungiyoyin.
Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Napoli, Mario De Laurantis, ya bayyana cewa zasu iya sayar da dan wasan bayan nasu amma sai an samu kungiyar da zata iya biyan abinda suke bukata.
Itama kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta bayyana bukatarta ta sayan dan wasan wanda a kwanakin baya ya bayyana cewa yana fatan barin kasar Italiya da buga wasa kuma tuni Napoli ta bayyana cewa a shirye take data sayar da dan wasan bayan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: