Hussain Sulaiman" />

Lokaci Ya Yi Da Al’ummar Kasar Nan Za Su Rungumi Zaman Lafiya Da Juna

Lokaci ya yi da al’ummar kasar nan za su rungumi zaman lafiya da juna batare da nuna banbancin kabila ko yare ba , matsawar ana son ci gaban da ake bukata .

Wannan baya ni yan fito ne daga bakin mai kishin son zaman lafiya dake Kano, Alhaji Mumuda Liman Zangon Kabo, a lokacin da yake zzantawa da manema labarai a Kano. Mamuda Liman ya nuna matukar bacin ransa game da tashin hankalin da aka samu tsakanin musulmai da kiristoci a jihar Kaduna wanda haka ya jawo asarar rayuka da dukiyon al’umma ciki har da wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Irin wadanna rashin zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu abin damuwa har wasu jihohi ana samu kamar Taraba da Jos da sauran jihohin arewacin kasar nan, wannan kuma na matukar barazana ga dorewar kasar nan. Matukar hakan ya ci gaba zai hana masu sha’awar shigowa kasar nan domin kafa kamfanoni ko kuma zuba jari, zai kuma kawo nakasu wajen samar da aikin ga matasa musamman wadanda suka kammala karatu.

Amma idan aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali zai baiwa masu kafa kanfanono da zu na jari sha’awar shigowa domin kafa kamfanoni, saboda haka ya zama wajibi al’ummar musulmi da kirista su yi hattara wajen tayar da rigingimu da sunan  addini ko kabilanci.

Kasashen da suka ci gaba irin su Amerka da Jamus da Chana da Faransa da zaman lafiya suka bunkasa ba da kashe kashe ko kone kone ba Mamuda Liman ya yi amfani da wannan dama da jawo hankulan matasa da cewa su daina yarda ana amfani da su wajen tayar da rigingimu, maimakon haka su fi mayar da hankalin su wajen neman ilimi ko kasuwanci da koyon sana’oin dogaro da kai .

Iyayen yara kuma su tabbatar sun rinka sanya idanu akan zirga zirgan yaran su ako da yaushe, domin wasu abubbuwan da yara ke aikatawa akwai gudunmawar iyaye aciki.Malaman addinin musulunci da na kirista tare da sarakuna suna da rawar da za su taka wajen fadakar da mabiyan su muhimmancin zaman lafiya da juna , abin kunya ne ace har yanzu ana samun rashin jituwa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinan guda biyu duk da kasan cewar suna zaune da juna shekaru aru aru dole sai an hada kai tare idan anma son cigaba

Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya baiwa kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali

Exit mobile version