Connect with us

RA'AYI

Lokaci Ya Yi Da Shugaba Buhari Zai Yi Garanbawul Ga Mukarrabansa –Giwa

Published

on

Wani basarake kuma jigo a siyasar Neja, Alhaji Muhammadu Awaisu Giwa (Wakilin Gbagyi-Nupe) ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari matakin gyarar fuskar da mukarrabansa suka tafka a karkashin ikon sa musamman na bin hukuncin kotu kan dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshimole. Domin idan bai yiwa tufkar gyaran fuska ba haka zai kare wa’adinsa bai iya aiwatar da komai ba, dattijon ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a minna juma’ar makon nan mai karewa.

Yanzu ba zaben 2023 ne a gaban mu, muna bukatar duk inda ya huje shugaba Buhari ya tabbatar ya dunke shi, domin al’umma sun sanya idanu suna kallon sa, shi kuma ya zauna an dabaibaye shi a na ta tafka barna da sunan shi, amma matakin da ya fara dauka yanzu muna da tabbacin ya kama hanyar gyara kurakuran da ake tafkawa kuma a kullun abin na ta cigaba. Bai yiwu wa mutumin da talakawa suka fito suka mara masa baya ya zura idanu a na son zuciya saboda bukatar wasu ‘yan tsirarun mutane marasa amana.

Lokaci bai kure masa ba, domin cikin watanni tara tsohon shugaba Abdussalam Abubakar yayi aka kafa jam’iyyun siyasa aka yi zabe har Allah ya baiwa PDP nasara, bayan shekaru sha shida tana mulki, cikin kalilan watanni jam’iyyun siyasa suka fito suka gamayya har shi shugaba Buharin ya samu nasara a APC, dan haka yana da shekaru uku a gabansa wanda zai iya anfani da su wajen share duk wani baragurbi dan samar da shugabanci mai inganci.

Tunda aka fara siyasa a kasar nan ban taba ganin irin salon mulkin Oshimole ba, inda ake karyawa yadda ake so, saboda haka dakatar da shi akan jagorancin wannan jam’iyyar hanya ce ta kawo gyara a tafiyar APC a kasar nan.

Yana da kyau yadda aka yi wannan a matakin tarayya a dawo a dubi jahohi, duk wani shugaban jam’iyya da ya taka rawa irin ta Oshimole a waje da shi, a samar da nagartattun mutane da zasu farfado da jam’iyyar dan samun tsarin siyasa mai inganci, yanzu dubi irin abin kunyar da aka rika tafkawa a Neja, daga matakin jiha har kananan hukumomi wanda shugabannin jam’iyyar suka mayar da kujerun su wajen yunkurin tara abin duniya ta hanyar dan ne nagartattun mutane da jama’a ke muradin su, aka rika kakabawa mutane ‘yan takarar da ba su suke bukata ba, suka mayar da jam’iyya aljihunsu sai yadda suka ga dama suke aiwatarwa.

Ya kamata yadda aka fara gyaran fuska a matakin jam’iyya duk wasu hukumomin gwamnati da aka tabbatar an yi rashin gaskiya a taba shi, domin hakan zai nunawa ‘yan kasar cewar an dauki turbar gyara.

‘Yan Najeriya Buhari suka sani ba APC ba, idan ba a samar da ginshikai ingantattu ba haka za a cigaba da tafiya cikin wannan yanayi, an baiwa mutane amana suna ganin kamar sun fi kowa. Dole duk wanda zai shugabanci kasar nan sai yayi damara in ba haka zai yi ta aza harshen gini da tuka, wanda ba za a je ko ina ba ya ginin ya rigizo, an ma shugabanni suka samu dama har sun wuce makadi da rawa, to ina gwaninta a nan, ina kwarewar, lokaci yayi da za a kawo karshen irin wadannan mutanen a tafiyar da mulkin kasar nan, domin ba su da alfanun da kwarewar da zai taimakawa kasar nan wajen samun cigaban da ake bukata.

Duk wanda aka san ya taka rawa a mulkin Oshimole ya zauna dan barnar ta isa haka, cigaba muke nema, a fitar da jama’a cikin kunci da halin lahaular da suke ciki haka nan.

Shekaru uku ne a gaban Buhari, lokaci yayi da zai yi anfani da su wajen kawo karshen zubar da jinin jama’a da sunan siyasa, a samar da turbar da za a hana duk wani dan ta’adda nunfasawa, ta hanyar samar da kwararrun mutanen da zasu taya shugaban kasa wannan aikin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: