Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kuma kaftin din kungiyar Lionel Messi, ya bayyana cewa bashi da inda yafi kungiyar Barcelona a rayuwarsa amma kuma lokaci yayi da yakamata ya bar kungiyar.
Duk da cewa burin dan wasa Messi na barin Barcelona a farkon wannan kakar bai cika ba amma dan wasan yana ganin lokaci yayi da zai fara tattaunawa da wasu daga cikin kungiyoyin da suke bibiyarsa duk da cewa har yanzu bai fara Magana da kowacce kungiya ba kawo yanzu.
A wata hira da Messi da manem alabarai Messi ya bayyana cewa shekara da shekaru a baya yana gayawa shugaban gudanarwar Barcelona na wancan lokaci Josep Maria Bartemue cewa yana son barin kungiyar amma shugaban yaki amincewa duk da cewa yana gaya masa cewa zai barshi ya tafi.
“Bartemeu ya dade yana yaudara ta saboda na dade ina gaya masa cewa inason barin Barcelona amma yana gayamin maganganu marasa dadi kuma yana gayamin zai bani damar tafiya ashe bansani ba yaudara ta yake” in ji Messi
A cikin watan Agustan daya gabata kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta so daukar dan wasa Lionel Messi daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, bayan da dan kwallon ya bukaci barin kungiyar sakamakon rashin jituwa da tsohon shugaban gudanarwar ta Barcelona.
Barcelona ta ci karo da cikas a kakar bara, bayan da ta kasa lashe kofi ko guda daya, bayan dukan kawo wuka da Bayern Munich ta yi mata a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League daci 8-2.
Kyaftin din tawagar na Argentina ya samu rashin jituwa da Josep Bartomeu – wanda ya ajiye aikin shugabantar Barcelona a cikin watan Oktoban daya gabata wanda hakan yasa dan wasan ya bukaci raba gari da kungiyar wadda ya fara bugawa wasa tun yana matashi.
Kwantiragin Messi zai kare a kungiyar Barcelona a karshen watan Yunin shekarar 2021, wanda hakan na nufi wata kungiyar za ta iya tattaunawa da shi da nufin daukar shi ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa.
Wannan dama ce idan Manchester City za ta yi amfani da ita wajen sake zawarcin kyaftin din Argentina sai dai wasu bayanai na cewa Manchester City ba za ta iya biyan Barcelona Yuro miliyan 50 ba, kudin da kungiyar za ta amince saboda halin matsi da cutar korona ta haddasa.
Ana ganin Manchester City za ta iya jira zuwa karshen kakar bana, lokacin da kwantiraginsa zai kare a Camp Nou kuma zai tafi ba tare da kungiyar ta Barcelona ta samu ko sisin kwabo ba sai dai kuma yawan albashin da yake dauka zai hana wannan ciniki.
Tuni dai Manchester City ta haura da zawarcin dan wasan saboda yana daukar yuro miliyan 100 wanda ba karamin kudi bane a halin yanzu da kungiyoyi suka talauce sakamakon annobar cutar Korona hakan yasa dole zasu hakura da daukar dan wasan.
Tuni dai aka bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar PSG ya fara shirye-shiryen tattaunawa da wakilan dan wasa Messi a cikin watan Janairu domin ganin ko zasu iya shawo kan dan wasan ya amince ya koma kasar Faransa da buga wasa.
Sai dai banda Manchester City, kungiyoyin Chelsea da Inter Milan da kungiyar Bayern Munchen duka sun nemi Messi sai dai a halin yanzu ana ganin PSG ce akan gaba wajen neman kaftin din na Barcelona da Argentina.