Connect with us

WASANNI

Lokaci Ya Yi Da Zan Bar Real Madrid –Kobacic

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Matteo Cobacic dan kasar Crotia ya bayyana cewa yanzu lokaci yayi daya kamata yabar kungiyar Real Madrid saboda baya samun buga wasanni akai-akai.
Dan wasan wanda yakoma Real Madrid daga kungiyar Inter Millan shekaru uku da suka gabata karkashin mai koyarwa Rafael Benitez ya buga wasanni 109 a kungiyar ta Real Madrid tun bayan komawarsa.
Kobacic mai shekaru 24 a duniya ya ce yanzu lokaci yayi daya kamata yaje kungiyar da zai dinga samun buga wasanni akai-akai saboda har yanzu shi matashin dan wasa ne kuma akwai karfi a jikinsa.
“Inason koda yaushe in dinga buga wasa saboda banason zaman benci gaba daya kuma babu dan wasan da yake son zaman benchi sai dai abune mai wahala matashin dan wasa kamata ya dinga samun buga wasanni dayawa a kungiya kamar Real Madrid” in ji Kobacic
Yaci gaba da cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid babbar kungiya ce wadda samun buga wasanni koda yaushe abune mai wahala saboda kowa babban dan wasa ne saboda haka yake ganin lokaci yayi da zai koma inda zai dinga buga wasanni akai akai.
Dan wasan dai kawo yanzu yanada ragowar kwantaragin shekara uku a kungiyar sannan ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin zakarun turai guda uku a jere.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: