Lokutan Samartaka Da ‘Yan Matanci

Yan’uwa a yauma zan dan yi bayani a kan wannan mau’du’in mai matukar

muhimmanci wato lokutan samrataka da ‘yan matanci dan tunatar da kaina dakuma yan’uwana matsayin wannan lokaci na samartaka. Idan Allah ya so.

Ma’anar Kalmar Samartaka Da ‘Yan matanci

Duk kusan daya ne muna iya cewa sa’annin juna ne samartaka wani lokaci ne da jinsin namiji yake tashen balagarsa, in mace na wannan shekarun sai a ce tana lokacin ‘yan matanci. Lokacin samartaka samari kan jin wasu dabi’u na daban

kamar su, matsanan ciyar sha’awa, sakamakon suna kan tashen balagar fari ne. Don haka a wannan lokaci shi ne wanda ya fi hadari ga rayuwar samari ko kuma ‘yan mata. Suna wasu irin dabi’u a cikin rayuwarsu kamar haka, jida kai, ganganci, son a hole, soyayya, kokari wajen aiki da kazar-kazar, tashan karfi, son gwaninta da burge mutane musammam ma mata sa annunsa.

Mata kuwa akwai irin na su suma kamar su son kwalliya, yanga, son kula maza samari, jin kai da jin isa, son girma daganin dai-dai take da kowa wato jin itama

Babbace da kuma tunanin saurayi ko na miji.

 

Hatsarin Da Ke Tattare Da Lokutan Samartaka Ko ‘Yan matanci

Yan’uwa akwai hatsarurruka manya a wannan matakin na samartaka in ba a sami kulawa ta musamma  wajen iyaye ko kuma wani mai tsawatawa ba.

A wannan lokutan ne saurayi kanfara zabar abun da yake so ya zama in malami ne na addini to tun yana saurayi za ku ga ya dukufa neman ilmi kuma yana wa addini hidima in kowa dan kasuwa ne anan ne za ku ga ya kama kasuwanci gadan-gadan.

A wannan lokutan ne ake koyan shaye-shayen kwayoyo da kayan maye idan aka hadu da mugayan abokai. A lokacin samartaka ne ake gina tsarin na rayuwa mai kyau ko marar kyau. A wannan lokacin ne ake samun dama dayawa a rayuwa sakamakon lokaci da ake dashi da kuma rashin nauyi a kai. Awannan lokaci ne abubuwa na sha’awa suka mamaye zuciya kamar mata, son a yi ado na kece raini idan ana samun kudi ai wani lokacin ma koda ba a samu, shi kenan sai ka ga inba an dace ba rayuwa ta munana.

 

Matsalolin Da Suke Addabar Samari

Akwai matsaloli masu tarin yawa da suke cutar da samari subata musu rayuwa koma hallakasu baki daya kamar su.

1. Rashin Sana’a Ko Hanyar Shigowar Kudi: Da zarar matashi bashi da sana’a ko wata hanyar da kudi yake shigo masa sai ku ga ya zama abun tausayi baya iya daga hanu a cikin abokansa sanannan koda yaushe yana cikin kunci, ko budurwa ma ba zai yi takirki ba sai marar aji. Wani saurayin lalaci ne ke sa yaki yin sana’ar, wani kuma rashin jari, wani kuma rashin horo da shauran su. Dan haka lallai matasa a tashi a yi sana’a don a nemi halak. Domin shi kadai ne hanyar da matashi zai dogara a halin da muke cikin a yanzu.

 

2. Soyayya: Soyayya ita ma na daya daga cikin abun dake kawo wa samari matsala a cikin wannan lokaci, sakamakon soyayya fal take da shashanci, shirme, takaici, bacin rai, takura, wahala, cinrai, fargaba, tunani, zancen zuci , sai kuma dan nishadi lokaci zuwa lokaci. Hakan tasa soyayya ke shafar tunanin samari da zarar saurayi ya fara soyayya za ka ga ya tattare hankulansa ya maida shi kan masoyiyarsa idan bai yi sa’ar budurwa me kirki ba ko surukai marasa kirki ba shi kenan sai su yi ta caja masa kai. Soyayya da sha’awa tabbas nasa samari yin ta addanci kamar kisan kai, fade da sauran su, a karshe su jefa rayuwarsu a mugun hali wanda bai dace ba.

 

3. karancin Ilmi: Shima wannan matsalace babba dake cutar da samari, domin ilmi shi ne hasken rayuwa kuma gishirin zaman duniya da ilmi ne ake tinkaho a yau

domin jahilci ciwone. Da zarar saurayi ya zama baida ilmi imma na addini ko kuma na zamani wato boko haka zai zama me karancin amfani ga al’umma, bai san kansa ba ballantana ya san wani harma ya ba shi shawara bai iya tsinana komai imam a kansa ko kuma ga al’umma. Dan haka matasa lallai a tashi a nemi ilimin addini dana zamani wato boko sosai ba ji ba gani, ka rage siyan sutturu ka sayi littafan addini,ko katara kudin rijista kafara karatu shi ne mafitarka a cikin wannan zamani.

 

4. Iyaye: Tabbas wadansu iyaye suna daya daga cikin wadanda suke ke haifar da matsala ga ‘ya’yansu samari. Da yawan iyaye sukan kasa sauke hakkokinsu wanda Allah S.W.T ya dora musu na kula da ‘ya‘yansu. Musali rashin adalci a tsakani mata guda biyu ko ‘ya’yaye, gallazawa ‘ya’yan kishiya, dorawa saurayi nauyin gida da zarar ya fara kawo karfi koda da uban nada rifin asiri, kin taimakawa saurayi ya yi sana’a koda yana da hankali, tilasamasa ya yi auren zumunci koda baya bukata, rashi bashi ingartaccen ilimi. Dukka wadannan matsaloline na iyaye dake shafar rayuwar samari a cikin wannan zamani. Nasiha ta ga iyaye lallai su ji tsoran Allah su sauke amanonin da Allah S.W.T ya ba su na ‘ya’yansu, dole kabawa danka tarbiyya, koda ya balaga akwai hakkinsa a kanka na kula dashi, bashi shawarwari, nasiha, inkana da wadata yimasa aure da wacce yake so, bashi jari idan kana da hali, sannan ka bashi ilmi. Ta haka ne zai ji kanka nan gaba.

 

5. Abokai bata Gari: Suma bata garin abokai nada tasiri sosai a kan samari tahanyar koya musu munanan dabi’u kamar sata, shaye-shaye, neman mata da dai shauran su. Dan haka lallai iyaye kusa ido a kan abokan ‘ya’yanku a koda yaushe.

Domin abokin barawo shima barawone kuma idan kana son ka san addinin mutum ko halinsa to ka san na abokinsa. Wallahi da yawan masu aikata munanan halaye kamar fade, shaye-shaye, zina za ka ga batagarin abokai ne suka koya musu. Dan haka aboki ka kiyayi abokai bata-gari a hankali a hankali za su bata ka idan baka an kara ba.

 

6. Jagoranci Munanan Malamai: Samarin Nijeriya musamman ma samarin Arewaci kashi 75 cikin dari masu son addini ne da kuma yima addinin hidima. Amma sai a samu wadansu muyagon malamai sun abatar da su hanya.

 

Exit mobile version