Connect with us

WASANNI

Lorey Ba Ya Taka Leda Kamar Yadda Ya Dace –  Kroos

Published

on

Dan wasan Jamus Toni Kroos ya ce Lorey Sane ba ya taka leda kamar yadda ya kamata, kuma dole ya kara matsa kaimi wajen gyara yadda yake buga wasa kamar yadda takwaran wasansa a tawagar kwallon kafar Jamus ke yi.

Sane, mai shekara 22, bai samu shiga cikin ‘yan wasan da suka buga wa Jamus gasar kofin duniya ba ,amma ya koma cikin tawagar Jamus din don buga wasan kasashen Turai inda kasarsa za ta kara da Faransa ranar Alhamis, da kuma wani wasan sada zumunci da Peru.

Amma tun da aka fara kakar bana Manchester City ba ta fara wasa da shi ba, kuma bai buga wa kungiyar ba ranar Asabar a wasan data buga na firimiya.

“A wasu lokuta za’aji kamar Leroy Sane bai damu ba ko munci wasa ko ba mu ci ba kuma wannan ba hali bane mai kyau ga dan wasa sannan mai koyarwa bazai yarda da hakan ba,” in ji Kroos .

“Dan wasa ne da yake da komai da kake bukata wajen kasacewa gwarzon dan wasa a duniya, amma a wasu lokuta dole ka gaya masa cewar yana bukatar kara matsa kaimi,” kamar yadda dan wasan tsakiyar Real Madrid din mai shekara 28 ya bayyana.

Sane ya ci kyautar kungiyar ‘yan wasa ta matashin da ya fi iya buga wasa a kakar 2017-18 inda ya ci kwallo 10 kuma ya taimaka aka ci kwallo 15 a gasar Firimiya.

Amma wasan minti 30 kawai ya buga wa City a wannan kakar bayan kungiyar tasa ta buga wasanni hudu inda tasamu nasara a wasa uku tayi canjaras a wasa daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: