Lukaku Zai Maka Everton Gaban Kotu

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Romelu Lukaku ya ce zai dauki matakin shari’a kan kalaman da shugaban tsohuwar kungiyarsa ta Everton, Farhad Moshiri ya yi kan dan kwallon.

Moshiri ya ce Lukaku ya yanke shawarar barin Everton ne bayan da ya samu wani sako daga matsafa na cewa kada yacigaba da zama a kungiyar

Lukaku ya koma Manchester United da buga wasa kan fam miliyan 75 a watan Yuni, bayan da bai amince da tayin tsawaita zamansa a Eberton din ba.

Wakilan Lukaku sun shaidawa manema labarai cewar, shawarar da Lukaku ya yanke ta koma wa United ba ta shafi sakon matsafan ba kuma dan wasan bashi da alaka da kowanne matsafi a duniya.

Moshiri yace sun gama tattaunawa dad an wasan akan zai cigaba da zama a kungiyar sai kawai mahaifiyarsa wadda taje wajen matsafi ta kirashi a waya inda ta gayamasa cewa kada ya zauna a kungiyar

Yaci gaba da cewa wannan dalili ne yasa dan wasan yaga bazai iya zaman kungiyar ba duk da kokarin da kungiyar tayi na ganin yaci gaba da zama a kungiyar na tsawon shekaru biyu.

 

Exit mobile version