Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Ma’adanai Da Karafa Za Su Iya Farfado Da Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista

Published

on

Ministan ma’adanai da karafuna Olamilekan Adegbite ya bayyana cewa, ma’adanai da karafuna su ne hanya mafi dacewa wajen samun kudaden shiga, sakamakon matsalolin tattalin arzikin da aka fuskanta saboda cutar Korona. Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta janyo masu zuwa jari daga Ingila da ma wasu sauran kasashen ketare, domin zuba jari a fannin ma’adanan Nijeriya.

A cewarsa, “ya kamata masu zuba jari daga kasar Ingila da wasu kasashen waje su zuba jai mai yawa a fannin ma’adanan kasan Nijeriya, domin samun gagarumar riba a cikin wannan bangaren.”

Ministan ya yi wannan jawabi ne wajen tattaunawar harkokin kasuwanci tsakanin Nijeriya da kasar Ingila wanda ya gudana ta yanar gizo. Ya kara da cewa, gwamnatin da ke mulkin a yanzu haka ta fara nemo hanyoyin magance matsalolin da suka addabi fannin. Ya ce, fannin ma’adanai da karafuna zai samar da hudaden shiga mai yawan gaske wanda ya fi na man fetur da kuma kara wa tattalin arzikin Nijeriya yawa da kashi uku daga cikin kudaden shigan da kasar nan ke samu.

“Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana kokarin magance matsalolin da fannin ma’adanai ke fuskanta da kuma farfado da fannin kasancewa an yi watsi da shi. Zai fi kyau mu yi kokarin gyara fannin ma’adanai, saboda a shekarar 1980 kafin samun man fetur fannin ya samar da kashi 5.6 daga cikin kudaden shiga na wannan kasa,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, fannin ne da ake zuba jari wanda zai bai wa Nijeriya damar samar da ayyukan yi da kuma kara samun kudaden shiga.

Tattaunawan mai taken zuba jari a Nijeriya wanda ya samu damar halartar shugaban hukumar fitar da kayayyakin daga Nijeiya, Olusegun Awolowo, wanda ya bayyana cewa, hukumarsa tana shawartar Nijeriya ta samar da wani shiri wanda zai bayar da damar fita da kayayyakin daga Nijeriya zuwa kasashen ketare wanda zai sa a rage dogaro da man fetur.

Shugabar hukumar NEPC, Misis Yewande Sadiku, ta bayyana cewa, wannan dama ce ta Nijeriya za ta yi amfani da ita wajen zuba jari da kuma farfado da tattalin arzikin kasar nan wanda ya durkushe sakamakon cutar Korona.

Shugabar wata mujalla da ake wallafawa, Misis Yinka Fayomi, ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa kokarin janyo masu zuba jari cikin sauki zuwa wannan kasa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: