Ma’aikata 3,000 el-Rufa’i Ya Kora Daga Aiki

Tallafin Gwamnatin Kaduna

Daga Auwal Mu’azu

Kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya ta ce kawo yanzu gwamnatin jihar ta kori ma’aikata kusan dubu uku daga bakin aiki.
kungiyar ta yi ikirarin cewa ma’aikatan wadanda galibi kanana ne an sallame su ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, inda ta bayyana rashin amincewarta tare da yin barazanar fara daukar mataki a kan lamarin muddin gwamnati ba ta sauya shawara ba.
Gwamnatin el-Rufa’i dai ta yi kaurin suna wajen sallamr ma’aikata daga bakin aikinsu a Najeriya, sai dai a wannan karon ta ce adadin bai kai haka ba.
Zaharaddin Lawan ya hada rahoton kan haka ya kuma tuntubi wadanda aka kora da kuma shugabannin kungiyar yan kwadago ta jihar.
Haka kuma ya tuntubi kwamishinan Kananan hukumomi na jihar Kadunan Alhaji Jafaru Sani, wanda ya yi Karin bayani kan matakin korar ma’aikatan

Exit mobile version