Ma’aikata Da ‘Yan Fansho Na Bogi Sun Jawo Wa Gwamnatin Bauchi Asarar  Naira Bilyan 1.062

Taki

 

Daga Khalid Idris Doya

 

Gwamnatin jihar Bauchi ta shelanta cewar ta yi ya bayyana cewar, hasarar kudade fiye da naira biliyan daya (N1.062) ta kwaroron aljifan ma’aikata da masu fansho na bogi tsakanin watan shida na shekara ta 2016 zuwa Janairun wannan shekara ta 2020.

 

Kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki, Umar Sanda Adamu shine ya sanar da hakan wa ‘yan jarida a Bauchi inda yake mai cewa ma’aikatan bogi da ‘yan fansho na bogi sun sanya gwamnati asara sosai wanda kuma tunin ta tashi tsaye domind dakile hakan.

 

Alhaji Umar Sanda Adamu ya ce a halin da ake ciki yanzu, ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati guda 668 sun gabatar da kundi da ya ke dauke da yawan ma’aikatan su, da kuma ragowar 13 da suke dab da gabatar wa.

 

Kwamishina Sanda Adamu ya bayar da tabbacin cewar, gwamnati tana aiki ka’in –da-na’in na mallakar sahihiyar matattara bayanai kan yawan ma’aikatan ta dangane da biyan albashi da fansho wa wadanda suka cancanta.

 

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Bauchi ta bijiro da tsare-tsaren cigaban jihar na tsawon shekaru biyar masu zuwa, wato daga shekara ta 2021 zuwa shekarar 2025, kamar yadda majalisar zartarwa ta zartar a zamanta na wannan makon a shekaran jiya.

 

Da ya ke yin tsokaci a wani taron manema labarai a garin Bauchi, fadar jihar, Kwamishinan kasafin kudade da tsare-tsaren kashe su, Dakta Aminu Hassan Gamawa ya ce majalisa ta amince da kudurin tsare-tsaren a zamanta wanda gwamnan jihar Bala Abdulkadir Mohammed ya jagoranta.

 

Dakta Aminu Gamawa ya bayyana cewar, tsare-tsaren bunkasa cigaban na jihar Bauchi ya bayar da fifito ne wa wasu muhimman fannonin cigaba da suka hada da fannin ilimi, aikin gona, ayyukan gine-gine, kiwon lafiya da samar da kwararrun ma’aikata wadanda za su zama jigo wa ayyukan.

 

Kwamishina Gamawa ya bayyana cewar, ma’aikatarsa ta gabatar wa majalisa kuduri ne akan tsare-tsare kashe kudade kan dabtarin kasafin kudade na shekarar da za a shiga ta 2021.

 

Ya kuma bayyana cewar, ma’aikatar sa za ta gudanar da taron fadakarwa ga jama’a tsare-tsaren dake cikin dabtarin kasafin kudi na shekarar ta 2021, domin bayar da gudummawarsu, kazalika kuma an bukaci ma’aikatu, hukumomi da sassa na gwamnati da su gaggauta kammala tsare-tsaren kashe kudaden na shekara mai zuwa domin gabatarwa wa majalisar dokoki ta jihar.

 

Kwamishinan na tsare-tsaren kashe kudade na gwamnati na jihar ya kuma ji takaicin yadda annobar Korona ta kawo tsaiko kan aiwatar da dabtarin kasafin kuDi na shekara ta 2020, kamar yadda aka tsara.

 

Dangane da sabunta tsarin birane a daukacin jihar Bauchi kuwa, Kwamishinan ayyuka da sufori na jihar Bauchi, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Mohammed, Chika Soron Bauchi, ya ce gwamnatin jihar bada jimawa ba zata bijiro ayyukan gina hanyoyi a cikin shiyyoyi guda uku na jihar Bauchi.

 

Shugaban Ma’aikata na jihar, Alhaji Aliyu Jibo, da kwamishinan kiwon lafiya, dana Kimiyya da Makamashi, Dakta Aliyu Mohammed Maigoro da Alhaji Umar Abubakar Sade suna daga cikin wadanda suka yi wa manema labarai bayyanai dangane da aikacen-aikacen ma’aikatun su.

Exit mobile version