Abubakar Abba" />

Ma’aikata Miliyan Takwas Ne Su Ka Yi Rijistar Fansho – NBS

Hukumar gididdiga ta kasa (NBS) ta sanar da cewar ma’aikata su 7,975,976 suka yi rijista a karkashin shirin fansho a farkon shekarar 2018 idan aka kwatanta da guda 7,823,911 da suka yi rijista tsakiyar shekarar 2017.

Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin kundin kadara na fansho da da kuma kudin da suka ajiye a asusun ajiya na (RSA) da hukumar ta fitar a ranar talata.

Acewar rahoton a cikin kundin kadara na fansho da da kuma kudin na farkon shekarar 2018, ya kai miliyan 7,943 sabanin naira miliyan 7,515 da aka samu a tsakiyar shekarar 2017.

Rahoton ya kara da gwamnatin tarayya ce tafi bayar da kaso mafi tsoka da ya kai kashi 48.61 bisa dari na jimlar kadara ta fansho , inda kadara ta asusun ajiya ya kai kashi 20.89

Acewar hukumar shiya ta cikin gida ta kai ce ta cikin gida ta kai kashi 9.25, inda kuma abinda hukumar ta zuba ya kai kashi 0.07.

Rahoton ya bayyana cewer, wadanda suka shiga sune masu shekara daga 30zuwa 39, inda sune suke da kashi mafi yawa da ya kai miliyan 2,986,752.

Rahoton ya kara da cewa, wadanda suke bi sune masu shekara daga 40zuwa 49, inda suka kai miliyan 2,203,123 sai kuma masui shekaru 50 zuwa 59inda suke da miliyan 1,430,180

Exit mobile version