Maigari Abdulrahman" />

Ma’aikata Sun Jadda Rokonsu Ga Buhari Kan Ya Taimaka Ya Sa Wa Dokar Karin Albashi Hannu Kafin Mayu

Ma’aikatan gwamnati a babban birnin tarayya sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya taimaka ya saka wa sabuwar dokar karin albashi da ‘yan majalisa su ka kai ma sa tun 27 ga watan Maris da ya gabata hannu.
Wasu daga cikin ma’aikatan da su ka zanta da kanfanin dillancin labarai na kasa NAN, sun nuna damuwar ssu kan tsaikon da Buhari ke yi wurin saka hannun, inda su ka ce, tsaikon na haifar ma su da yawan damuwa da tunani na ba-gaira-ba-dalili.
Wata ma’aikaciya mazauna Abuja, Madam Kema Nwokedi cewa ta yi, ya kamata Buhari ya ida kammala aikin kwamitin karin albashi da su ka faro, ta hanyar sanya wa sabuwar dokar hannu.
Madam din, ta roki shi da ya duba halin wahalhalu na tattalin arziki, ya saka hannu a kan dokar domin kawo karshen wahalar ma’aikata.
“Ka sanya farin ciki a zukatan yan Nijeriya ta hanyar yi mana kyauta a hutun ‘easter’ da karin albashi,” da take roko.
Haka shi ma, wani ma’aikacin, Abdullahi Sani, ya roki da ya sanyayawa ma’aikata da saka wa dokar hannu kafin farkon watan Mayu mai kamawa.
Mista Dayo Adedayo, ma’aikaci a ma’aikatar Masana’antu da kasuwanci, cewa ya yi, sanya wa dokar hannu taimakon ma’aikata ne. Tsaikon sa hannun na kara tsanani ga ma’aikata maras misaltuwa, domin albashin ma’aikata a yanzu, ba ya iya daukar lalurorinsu, inji shi.
Ko a satin da ya gabata dai, kungiyar kwadago ta kasa ta roki shugaban kasa Buhari, da ya dubi halin da ma’aikata ke ciki na yanayi, ya saka wa dokar hannu.
Bayan daukar dogon lokaci a na taka leda tsakanin kungiyar kwadago da Gwamnatin tarayya kan karin albashi, daga karshe kwamitin da aka kafa sun cimma matsaya na naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi, inda yan majalisun tarayya na kasa suka amince, kuma su ka aikewa shugaban kasa domin sa hannu. Abin da ya yi saura yanzu, sa hannun Buhari, abin da ma’aikata ke ta saurare kenan.

Exit mobile version