Khalid Idris Doya" />

Ma’aikatan Bauchi 1,800 Sun Rubuta Jarrabawar Karin Girma

Ma’aikatan Bauchi

Shugaban ma’aikata na jihar Bauchi, Aliyu Jibo ya shaida cewar a kokarin gwamnatin jihar na inganta aiki da tabbatar da lamura suna tafiya daidai, ta himmatu wajen horaswa ga daukacin ma’aikatan jihar domin tabbatar da ingancin aiki a kowani lokaci.

 

Shugaban ma’aikatan wanda ya samu wakilcin Yusuf Karamba, ya shaida a ranar Talata yayin bude taron jarabawar karin girma wa ma’aikatan jihar sama da dubu 1,800 na 2020.

 

Taron kwanaki biyu na horaswar gwamnatin jihar ce ta shirya da hadin guiwar kamfanin Dugge domin kara wa ma’aikatan ilimi tare da koyar da su dabarun ririta dukiya da tafiyar da ayyukan gwamnati yadda ya dace a ofisoshin da suke aiki.

 

Alhaji Aliyu Jibo ya ce, a shekarar 2009 ne gwamnatin jihar ta bijiro da wanan tsarin wanda zuwa yanzu ya yi amannar cewa an samu muhimman nasarori wajen tabbatar da tsaftacewa da kyautata sashin gudanar da aiki da bin dokoki da ka’idojin aiki dukka domin nagartar aiki.

Jibo ya ce, su na shirya jarabarwar karin girmar ne domin duba hazaka da kwazon ma’aikata domin tabbatar da ajiye kowani mutum a ofishin da ya dace domin tabbatar da ayyuka su na tafiya bisa dacewa.

 

Ya ce, kari kan natijar taron biyar, ma’aikatan su na kara samun ilimi sosai a kan kwarewarsu da kuma dabarun tafiyar da ayyuka wanda zai basu damar cinye jarabawar neman karin girma cikin sauki.

 

Ya shaida cewar a shekarun baya, kusan kaso 80 cikin 100 na ma’aikatan da suke samun horo daga baya su zana jarabawar karin girman su na cinye jarabawarsu ba tare da samun tangarda ba, ya na mai nuna kwarin guiwarsa a wanan shekarar ma za a samu cimma wannan nasarar.

Alhaji Aliyu Jibo ya shaida cewar wannan jarabawa na karin girman dukka su na daga cikin kokarin gwamnati na tabbatar da walwala da jin dadin ma’aikatan jihar ne, yana mai bayanin cewar ba kawai an shirya musu horon don su tsalllake gwajin da ake son musu ba ne, har ma da kara musu gogewa da sanin dabarun tafiyar da aiki domin aikin gwamnati take tafiya yadda ya dace.

Ya ce, ilimin da aka baiwa ma’aikatan zai ba su damar cinye jarabawarda za a yi muku zalla ba ne, a’a zai taimakesu wajen aiwatar da ayyukan da suke gabansu na yau da kullum.

Shugaban ma’aikatan ya shaida cewar gwamnatin jihar Bauchi tana kokarinta wajen kyautata wa ma’aikata don haka ne ya nemi su ma ma’aikatan su tashi tsaye wajen saka wa gwamnatin da yin aiki tukuru domin jama’a.

Babban Daraktan kamfanin da aka daura wa alhakin shiryawa da kuma tsara jarabawar, Alhaji Gambo Magaji ya shaida cewar an tsara yadda kowani ma’aikaci zai samu zarafin kyautata aikinsa da kuma samun karin girma ba tare da ya sha wuya ba, ya bayyana cewar horon da kuma jarabawar ya ta’allaka ne kan ayyukan da ma’aikatan suke gudanarwa a ofishinsu na yau da kullum.

Ya yi bayanin cewar ana tsara jarabawa ne ba don a wahalar da jama’a ba ne, illa don a ga irin fahimtar dalibai.

Alhaji Gambo Magaji ya tabbatar da cewar dukkanin ababen da suka dace wajen gudanar da jarabawar karin girmar an samar da su, ya yi fatan nasara wa dukkanin ma’aikatan da suke amsar horon a hanunsu kawo yanzu.

 

Exit mobile version