Ma’aikatan NHIS Sun Jaddada Goyon Baya Ga Sakataren Hukumar

Wasu daga cikin ma’aikatan hukumar da ke bayar da Inshuran lafiya ta Nijeriya (NHIS), a shekarani jiya ne suka jaddada aniyarsu na ci gaba da mara goyon baya wa babban Sakataren hukumar Inshuran Lafiya Farfesa Usman Yusuf wadda aka dawo da shi mukaminsa na sakataren hukumar biyo bayan zarginsa sama da fadi da dukiyar hukumar.

Da suke jawabi wa manema labaru karin bayani kan dalilainsu na mara masa baya, a shalkwatan NHIS da ke Abuja, Uchenna Ewelike, da kuma Mohammad Shehu Gajo, wadanda suke karkashin sashin kula da ma’aikatan NHIS, sun nuna karin guiwarsu ga Usman Yusuf hade da bayyana sa a matsayin wadda zai cire kitse a wuta.

Sun bukaci dukkanin ma’aikatan hukumar bayar da Inshuran Lafiya  da su ci gaba tafiyar da harkokin aikinsu kamar yadda suka saba ba tare da kokarin kawo rudani ko hargitsi gami da zargin juna ba, hade kuma da kaurace wa biye wa dukkanin masu kokarin haifar da rikici.

Har-ila-yau, sun kuma bukaci bangarorin jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen yin aikinsu da bin dokokin da aikinsu da ya shimfida musu don hukunta dukkanin wani ko gungun jama’an da suke kokarin kawo rudani gami da neman haddasa tashin-tashi a tsakanin ma’aikatan hukumar a yayin da suke kan aiyukansu.

Suka ce, “a matsayinmu na ma’aikatan gwamnati, muna da ka’idojin da kuma sharudan da aikinmu da ya gindaya mana, don haka ba za mu amince da kokarin wasu na kawo rudani wadanda manufarsu baiwa cin hanci da rashwa gindin zama ne, za mu taba basu kofa ba, don haka za mu ci gaba da yin aikinmu yadda ya dace”.

Sannan kuma, sun yi kira ga bangaren kungiyar ma’aikatan lafiya, MHWN da ASCSN da su yi kokarin dinke barakar da ke akwai a tsakanin bangarorin d suke karkashin hukumar NHIS hade da samar da ci gaba mai ma’ana domin tafiyar da aiki yadda ya dace, kana sun kuma shawacesu daure su ci gaba da bayar da gudunmawarsu domin taimaka wa jama’an kasa.

Uchenna Ewelike ya gode wa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a bisa wanke babban sakataren hukumar Inshuran lafiya ta Nijeriya Farfesa Yusuf bisa zargin cin hanci da rashawa hade da wawuson dukiyar hukumar da aka yi zarginsa da yi.

A makon jiya ne dai wasu ‘ya’yan kungiyar da wasu manyan ma’aikatan lafiya suka gudanar da wani zanga-zangar lumana kan kin amincewa dawo da Farfesa Yusuf kujerarsa ta sakataren hukumar Inshuran lafiya biyo bayan zargin da hukumar EFCC ta yi masa na sama da fadi da dukiyar hukumar.

 

 

Exit mobile version