Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Ma’aikatar Gona Ta Bauchi Ta Kaddamar Da Dashen Itace

by Tayo Adelaja
September 20, 2017
in RAHOTANNI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Ma’aikatar gona da albakatun kasa ta jihar Bauchi ta kaddamar da fara dashin itatuwan shuka wadanda za su taimaka wa jihar don kareta daga fadawa kwararowar hamada. An fara kaddamar da aikin ne a garin Lariye da ke karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi, kaddamarwar wanda ya gudana a jiya.

samndaads

A yayin kaddamarwar gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar, wanda babban mai tallafa masa kan harkokin tsaro Janar Ladan Yusuf Mai Ritaya ya ce a bisa yanda suka saba duk shekara ne ya sanya suka gudanar da wannan aikin na dashen itatuwa. Ya ce gwamnatin jihar Bauchi ta himmatu wajen inganta sha’anin noma a jihar a bisa haka ne ma gwamatin ta kawo shirye-shirye da tsare-tsare domin inganta harkar da suka shafi noman.

Ya ce, wannan dashen itatuwan zai kare jihar ne daga fadawa matsalar kwarauwar hamada da sauran matsalolin da hakan ke jawowa.

Gwamnan ya ce zai ci gaba da mara bawa wa baturan gona domin a samu kaiwa ga nasarar indata harkar ta noma a fadin jihar ganin muhimmancin da hakan ke da shi a tsakanin al’umma. Ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar zata sanya ido sosai kan lamarin itatuwa da shokikin jihar.

A hirasa da manema labaru kan shirin, babban sakatare a hukumar gona da albarkatun kasa Dakta Bala Musa Lukshi ya bayyana cewar kashi saba’in na al’umman jihar Bauchi manoma ne, a bisa gaka ne suke bada himma da kuma kulawa ta musamman wa manoma da harkar noma domin inganta sha’ain “mun raba itatuwan da aka saba rabawa kullu, amma a wannan karon mun kara itatuwa biyu Dabino da kuma kwakwan manja. Su wadannan itatuwan biyun da gwamnatin jihar Bauchi ta sanyo amfanin da za su yi wa jihar Bauchi baya misaltuwa, za su kare jihar daga kwararowar hamada, musamman shi dabino yana da juriya wajen kare kwararuwar hamada, sannan shi dabino din nan zai yi ‘ya’ya zai kuma samar da abinci, kun ga, ga aikin yi zai samu ga abinci da za samar wa jihar haka shi ma kwakwan manja. Haka sauran itatuwan da muka kaddamar da rabawa a yau kowanne yana da na sa muhimmancin da zai taimaki jihar nan daga kwararuwar hamada”. In ji babban Sakataren

Lukshi ya ce, kimanin itatuwa kala daban-daban da adadinsu ya kai dubu shida da dari biyu ne 62,200 ne za a shuka a fadin jihar ta Bauchi. An kiyasce cewar nan da wata uku za a fara cin moriyar wasu daga cikin itatuwar irin su dabino da sauransu, inda Sakaraen ya ce irin itatuwar na zamani gwamnatin ta sayo domin inganta wannan shirin.

A nasa jawabin Sarkin Katagum, Alhaju Muhammad Kabir Umar wanda, Sarkin Yakin Katagum Alhaji Abubakar Yalwa ya bayyana muhimmancin da wannan dashen zai kawo wa al’ummarsu talakawar wannan yankin, inda ya jinjina wa kokarin gwamnan jihar Bauchi na inganta rayuwar al’umman yankin.

Sarkin ya ce “wannan dashen zai taimaka wajen dakile kwararuwar hamada, sannan itatuwa ne wadanda suke da muhimmanci a garemu. Don haka ita wannan kasar tamu”.

Sarkin sai ya yi kira ga jama’arsa da su ci gaba da bada himma kan noma da kiwo. Sai ya sha alwashin bada goyon baya da sanya ido domin kiyaye wadannan shukokin. “ina kuma kira ga jama’ana da su tabbatar da sun kiyaye wannan itatuwan domin cin moriyarsu. na ji dadi da yanda na ga wannan aikin na kaddamar da dashen ya gudana a wannan kauyen, mun gode da kokarin gwamnatin jihar nan”. A cewarsa

Da yake zantawa da wakilinmu, wakilin shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi a yayin taron Muktar A. Sulaiman ya shaida cewar shi dashen itatuwa na da matukar muhimmanci a addinance “Manzo ya ce idan ka dasa bishiya kana da lada, sannan wannan itatuwan za su taimaki al’umma kan ta fuskoki da daman gaske. shi mai girma gwamna a kullum yana damuwa ya ga yanda zai shawo kan matsalar hamada. shi dashen itatuwa zai taimaka maka wajen tattalin arzikinka, zai kuma kare maka hamadanka da kuma baka isashen itacen da zaka sara domin dafa abinci”. In ji shi.

Wakiinmu ya nakalto mana cewar nan take manyan baki da sarakuna iyayen kasa suka yi na’am da shirin inda suka jagoranci fara sanya itatuwan a muhallan da aka ware domin yin shukan. Jama’an yankin da aka kaddamar da aikin a wajensu sun nuna matukar jin dadinsu da wannan shirin na inganta sha’anin noma sai suka nemi gwamnatin ta ci gaba da taimaka musu domin samun cin moriyar romon Dimokradiyya a jihar. Daga bisani dai an rabar da irin shukokin ga jama’a domin su shuka a muhallansu da sauran wuraren da suka dace.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Jama’ar Yobe Sun Bayyana Gamsuwar Su Da LEADERSHIP A Yau

Next Post

Kimiyya: Illolin Sa Hotunan Iyalanku A Shafukan Sada Zumunta

RelatedPosts

Gina Hanyar Ruwa: Babu Kudin Kowa A Cikin Wannan Babban Aiki, Inji Mai Turaka

Gina Hanyar Ruwa: Babu Kudin Kowa A Cikin Wannan Babban Aiki, Inji Mai Turaka

by Daurawa Daurawa
8 hours ago
0

Mai taimakawa gwamna Masari akan wayar da kan jama’a akan...

’Yan Sandan Kano Sun Cafke Mace Mai Garkuwa Da Mutane

’Yan Sandan Kano Sun Cafke Mace Mai Garkuwa Da Mutane

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta shaida cewar wata mace...

Ta’aziyar Rasuwar Sam Nda Isaiah

Sam Nda-Isaiah Ya Rasu Lokacin Da Ake Tsananin Bukatar Gudunmawarsa – Jami’ar Jos

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Shugabannin jami’ar Jos sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da...

Next Post

Kimiyya: Illolin Sa Hotunan Iyalanku A Shafukan Sada Zumunta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version