A yau Laraba, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanya wasu kamfanoni 8 na yankin Taiwan cikin jerin sunayen wadanda aka takaita sayar muku kayayyaki.
Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar ta ce, an dauki matakin ne domin kiyaye tsaron kasa da kare muradunta da kuma cika wajibcin hakkin kasa da kasa kamar hana yaduwar abubuwa masu cutarwa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)