Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Ma’aikatar yada labaran Jihar Kano za ta yi aiki tare da dukkan masu fatan taimakawa wajen magance matsalar karacin abinci mai gina jiki a Jihar Kano.
Kwamishinan Ma’aikatar yada labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ne ya bayyana haka a taro tattaunawar da kungiyoyin sa kai dake duba ma’aunin abinci mai gina jiki a Nijeriya (CS-SUNN) da aka gudanar a ofishinsa. Kamar yadda Jami’in yada labaran ma’aikatar Sani Abba Yola ya shaidawa LEADERSHIP A YAU.
Kwamishinan, wanda Babban Sakatare a Ma’akatar, Usman Bala Muhammad, ya wakilta yace, dabarun sadarwar da ake fatan aiwatarwa za su taimaka wajen samun nasarar yakin da ake da matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Usman Bala ya kara da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki da aka yi watsi da shi sakamakon mutane sunfi mayar da hankali wajen abubuwan da ake iya gani a zahiri dake zaman kalubale ga harkokin lafiya, duk da cewa karancin abinci mai gina jiki ke haifar da mummunar illa a Kasarnan. Babban sakataren ya ci gaba da cewa matsalar a hankali na illata makomar dandazon al’ummar Jihar Kano da kasa baki daya.
Ya ce, Ma’aikatar na cikin tsarin matakan da ake kokarin aiwatarwa sannan kuma tana sane da batun abinci mai gina jiki lamari dake bukatar kulawar gaske, ya kara da cewa ya kamata a samar da wani kasafi kan wannan shiri a wannan ma’aikata.
Daga nan sai babban sakataren ya tabbatar masu da cewa ma’aikatar zata samar da jami’i guda kan lamarin karancin abinci mai gina jiki tare da yin nazarin halin da ake ciki domin samun nasarar shirin.
Tunda farko anasa jawabin, shugaban kwamitin kungiyoyin sa kan a harkar abinci mai gina jiki a kasar nan, Mr. Innocent Ekene ya bayyana cewa bayanai sun nuna cewa kashi 37% na yaran Jihar Kano na fama da irin wannan matsala wadda kuma tana da hadari kwarai ga cigaban tattalin arziki.
Shugaban ya kuma bukaci ma’aikatar yada labaran ta bujiro da wani shirin wayar da kai ta kafafen yada labarai domin fadakar da al’ummar Kano, Musamman wadanda ke zaune a karkara kan muhimmancin ingantaccen abinci mai gina jiki wanda ana iya samun sa wuraren da suke zaune.