Ma’anar Azumi A Musulunci (2)

Cigaba da bayani cikin littafin Guziri Ga Mai Azumin Watan Ramadana, wallafar Ibrahim Garba Nayaya

Satin da ya gabata, mun dan yi tsokaci game da ma’anar Azumi da abubuwan da suka shafi daukar Azumin. Ci gaba da bayaninmu a wannan mako, za mu tattauna a kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi Azumin watan Ramadan. Kar a manta dai, wadannan bayanai na nakalto su ne cikin littafin da Allah ya nuface ni da rubutawa. A sha karatu lafiya.

 

Falalar Azumin Watan Ramadan

Azumin watan Ramadana na da falala mai yawa, daga cikin falalar sun hada da:

 1. Azumi garkuwa ne. Manzon Allah S.A.W ya umarci wanda sha’awar aure ta yi tsanani gare shi da ya yi azumi, sai ya sanya azumin garkuwa ne gaa sha’awar, domin cewa shi azumi yana kange gabobi daga sha’awa.
 2. Azumi sababin shiga Aljanna ne, sannan kuma yana nesantar da bawa daga wuta, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abu Umamata R.A ya ce “Ya Manzon Allah S.A.W shiryar da ni kan aikin da zai kai ni ga shiga Aljanna”. Sai Manzon Allah S.A.W ya ce “Na hore ka da yin azumi, ba shi da tamka”. (Imam Ahmad 5/255-258. Ibnu Hibban 929).

Haka zalika, ya zo cikin hadisin da Imam Bazzar ya fitar cikin littafinsa cewa, Manzon Allah S.A.W ya ce da Huzaifah, “Ya Huzaifa, duk wanda ya cika da azumin yini daya mai nufin yardar Allah, Allah zai shigar da shi Aljannah”.

Game da nesantar da bawa daga wuta kuwa, Manzon Allah S.A.W ya ce “Babu wani bawa da zai yi azumi na kwana daya domin neman yardar Allah, face Allah ya nesantar da fuskarsa daga wuta tsawon shekaru saba’in”. (Bukhari, 6/35. Muslim, 1153).

A hadisin da Tirmizi ya fitar, cewa ya yi “Duk wanda ya yi azumin kwana daya domin neman yardar Allah, Allah zai sanya tazara tsakaninsa da wuta kamar tazarar sama zuwa kasa”.

A wani hadisin kuma ya ce “Azumi garkuwa ne da bawa zai kare kansa daga wuta”. (Imam Ahmad 3/241).

 1. Ana sakanyawa mai azumi da lada ba tare da kididdiga ba.
 2. Mai azumi yana da farin ciki biyu. Manzon Allah S.A.W ya ambata cikin wani hadisi cewa, “……. Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: idan ya yi buda-baki yana da farin ciki, haka idan ya hadu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa”. (Bukhari 1805, Muslim 163
 3. Warin bakin mai azumi ya fi turaren almiski kamshi a wajen Allah. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira R.A cewa, Manzon Allah S.A.W ya ce, “Dukkan aikin dan’Adam a gare shi ne, ban da azumi, domin Nawa ne kuma ni zan sakanya masa, azumi garkuwa ne. Idan ya kasance ranar azumin dayanku, to kada ya yi batsa, kada ya yi jahilci (shirme), idan wani ya zage shi ko ya neme shi da fada, to ya ce masa “Ni azumi nake yi”. Na rantse da wanda ran Muhammad ke hannunSa, warin bakin mai azumi ya fi turaren Almiski kamshi a wajen Allah. Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: idan ya yi buda baki yana da farin ciki, haka idan ya hadu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa”. (Bukhari 1805, Muslim 163).
 4. Azumi da Alkur’ani suna ceton ma’abocinsu, kamar yadda ya zo cikin hadisi cewa, Manzon Allah S.A.W ya ce “Azumi da Alkur’ani za su ceci bawa ranar Kiyama, azumi zai ce: Ya Ubangiji, na hana shi abinci da sha’awarsa, Ka ba ni cetonsa…………….”.
 5. Azumi yana kankare zunubai, Bukhari da Muslim sun fitar da hadisi cikin hadisin Huzaifata Bin Yaman R.A cewa, Umar Bin Khaddab R.A ya ce, “Wane ne wanda ya kiyaye hadisin Manzon Allah S.A.W wanda ya yi magana a kan fitina? Sai Huzaifa ya ce, “Ni ne, na ji Manzon Allah S.A.W yana cewa, “Fitinar da mutum zai samu a cikin iyalansa, da dukiyarsa, da makwancinsa, sallah da azumi da sadaka suna kankare su”.
 6. Kofar Rayyan ta masu azumi ce, kamar yadda ya zo a hadisin Sahal Ibn Sa’ad R.A cewa, Manzon Allah S.A.W ya ce, “Tabbas a cikin Aljanna akwai wata kofa, ana kiranta Rayyan, masu azumi ne za su shige ta ranar Kiyama, babu wanda zai shige ta sai su, kuma idan suka shige ta za a rufe ta babu wanda zai kara shiga. Kuma duk wanda ya shiga zai sha ruwa, kuma duk wanda ya sha ruwan ba zai kara kishirwa ba har abada”. (Bukhari 4/95, Muslim 1/52).

 

Sannan shi ma watan Ramadana yana da wasu falaloli da ya kebanta da su koma bayan sauran watanni da ba shi ba, cikin falalolin akwai:

 1. A cikinsa Allah ya saukar da Alkur’ani daga Lauhul Mahfuz, zuwa saman duniya.
 2. Wata ne da ake daure shaidanu, aiyukan sharri suna karanci a ban-kasa. Manzon Allah S.A.W ya ce; “Idan watan Ramadan ya zo, sai a budde kofofin Aljanna, sannan a rufe kofofin wuta, kuma a kulle shaidanu”. (Bukhari 4/97, Muslim 2/757).

Dukkan wannan yana kammaluwa daga lokacin da daren farko na wata mai albarka ya shigo, saboda fadin Manzon Allah S.A.W cewa; “Idan daren farko na Ramadana ya kasance, sai a kulle shaidanu da kangararrun aljanu, a rufe kofofin wuta, babu wadda za a bari daga cikinta, a bude kofofin Aljanna ba za a bar ko daya a rufe ba. Sai wani mai kira ya yi kira; “Ya mai neman alheri matso kusa, Ya mai neman sharri yi nesa! Kuma Allah yana da wasu ‘yantattu daga wuta, wannan kuwa yana faruwa a kowanne dare”. (Tirmizi 682, Ibnu Majah 1642).

 1. A cikinsa ne ake samun dare mafi daraja, wato Daren Lailatul Kadri. Anas Ibn Malik R.A ya ce, Manzon Allah S.A.W ya ce, “Lalle wannan wata na Ramadana, hakika ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin dake cikinsa), hakika an haramta masa alheri dukansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa sai wanda ba shi da rabo”. (Sunan Ibn Majah 1644).
 2. Amsar addu’a da kuma ‘yanta bayi daga wuta a kowanne dare cikin watan Ramadana.
 3. Gafarta zunubai, kamar yadda ya zo cikin hadisin da Manzon Allah S.A.W cewa, ya hau minbari sai ya ce, “Amin! Amin!! Amin!!!”. Sai aka tambaye Shi, sai ya ce “Hakika Jibrilu AS ya zo ya ce mini: “Duk wanda ya riski watan Ramadan bai yi abin da za a gafarta masa ba, har aka shigar da shi wuta, to Allah ya nisantar da shi daga rahamarSa,”. Ka ce “Amin”. Sai Na ce “Amin”…………..(Imam Ahmad 2/246).

 

 

Exit mobile version