Munkaila Abdullah" />

Mabukata 561 Sun Amfana Da Zakkar Naira Milyan Biyu A Masarautar Kazaure

Masarautar Kazaure

Kwamatin zakka na masarautar Kazaure ya raba zakar kudi naira miliyan biyu ga mabukata 561.

Shugaban kwamatin zakkah na masarautar, Alh Bala Mohd wadda Ma ajin kwamatin Alhaji Ilu suleiman ya wakil ta shi ya bayyana haka a tasting kaddamar da rabon zakkar.
Ya ce, mabukatan su kimanin 561 an  zakulosu daga  gundumomi tara dake karkashin masarautar ta Kazaure.
Shugaban kwamatin ya kara da cewa, zakkar wadda wani bawon Allah ya bayar za a bada ita ga asibitoci 6 dake a yankin masarautar wanda suka hada da babban asibitin kazaure da kuma asibitin Satire da ke kazaure.
Haka kuma, ya kara da cewar mabukata 150 ne zasu amfana da naira dubu 3 a kowacce gunduma.
Shi kuwa sarkin yaran kazaure Alhaji yusuf kira yayi ga mabukatan da suyi amfani da zakkar da a ka ba su ta hanyar da ya dace domin amfaninsu da iyalinsu baki daya.

Exit mobile version