CRI Hausa" />

Macao Za Ta Nace Ga Tsarin ‘Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu’

Kantonman yankin musamman na Macao na biyar, He Yicheng ya shedawa manema labarai na CMG cewa, Macao za ta nace ga tsarin “kasa daya mai tsarin mulki biyu” da amfani da damammaki masu kyau na bunkasuwar yankin mashigin tekun Guangdong da Hongkong da Macao wato GBA.
He ya jaddada cewa, yayin da ake aiwatar da tsarin “kasa daya mai tsarin mulki biyu”, abin dake gaban komai shi ne kasa daya, tilas ne a tabbatar da tsarin mulki da doka ta musamman na yankin, sannan a gudanar da shi a yankin Macao karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya yadda ya kamata cikin dogon lokaci.

Ban da wannan kuma, He ya nuna cewa, kafin dawowar yankin hannun babban yanki, Macao ta taba fuskantar koma bayan tattalin arziki, lamarin da ya haifar da tashe-tashen hankula, kowa ya dandani dacin lamarin, hakan ya sa aka cimma matsaya daya wajen tabbatar da kwanciyar hankalin yankin. Ya zuwa yanzu, an cika shekaru 20 da dawowar babban yankin, Macao na samun bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a yadda ya kamata, haka kuma matsayin siyasa na jama’arta na ingantuwa, saboda ana iya shiga harkokin kasa ta tsarin “Taruka biyu” a matsayin jama’ar kasar Sin.
Dadin dadawa, He ya ce, Macao na samun goyon baya daga gwamnatin tsakiya da jama’ar babban yankin, ya kamata ta yi amfani da zarafi mai kyau don samun bunkasuwar GBA, ta hanyar daidaita matsayinsa da yin amfani da babbar kasuwar babban yanki da kara tuntuba da hadin kai da babban yankin.

(Mai Fassarawa: Amina Xu daga CRI Hausa)

Exit mobile version