Mace Ko Namiji: Wa Ya fi Bukatar Kulawa?

Mafi yawancin mata a wannan zamani sun tafi akan cewa mace ce kadai ke bukatar kulawa wajen saurayinta ko kuma mai gidan ta musamman mata kabilar hausa wanda so da dama hakan ke haifar musu da gagarumar matsala cikin zamantakewar su tsakaninsu da samarin su ko mazajen su na sunna.

Wannan babbar kalubale ne garemu da muke fuskanta, wanda a halin yanzu ya zame mana matsala a tsakaninmu, har ila yau wannan gagarumar matsala na taka muhimmiyar rawa wajen rushe dangantakar dake tsakaninmu da abokan zaman mu.

Wannan abune dana dade ina tinanin nayi dan takaitaccen rubutu akan shi a matsayin gudummuwa ta koda hakan zai sa hankalin mu ya karkato izuwa gare shi.

A zahirin gaskiya bai kamata ace mata su tafi akan ra’ayinsu na cewa su kadai ke bukatar kulawa wajen samari ko mazajensu ba, wannan gurguwar tinani ne wanda ya saba ma shari’a, abune wanda koda ace hankali kika sa ki ka zurfafa tunani kinsan bai dace ba, saboda shi namiji ba a tankwara shi da karfi haka, ako ina yake yana kasancewa ne a namijin shi, ma’ana baya yarda ya kasance shi ake ba umurni saidai shi ya bada, sannan zuciyar namiji na bukatar lalama cikin sanyi kamar yanda mace take domin kowace zuciya na bukatar mai kyautata mata ne, wannan maganar sau da dama wadansu matan na tunanin nasu zuciyar ne kadai ke bukatar haka wanda kuma hakan ba daidai bane.

Babu yanda za ayi ace kina tare da saurayin ki ko maigidan ki ace kullum saidai ya kyautata miki ba tare da kina saka mishi da mafi alkhairi ko nuna godiyarki da jindadin ki akan hakan ba, hasali ma so da dama wasu matan na ganin babu wata bukata ta yin godiya ko nuna farin cikin su kan wata kyautatawa da mazajen su sukai musu ba, suna ganin cewa nauyi ne daya rataya akan su cewa dole ne su biya musu duka bukatunsu su kuma yi musu dukkan abinda suke so, saboda haka alhaki ne daya rataya a wuyar su dole kuma su sauke.

Wasu kebabbun ‘yan matan kuma mafi rinjayen su sun dora ma kansu girman kai ta yanda baza su taba nuna ma samarinsu kulawa ko wani abu daya danganci hakan ba, suna ganin cewa ba sune ya kamata suyi hakan ba don haka sunfi karfin suyi, hasali ma a mafi yawan lokuta sai su dinga nuna halin ko in kula ga samarin nasu. Da yawa kuma suna hakan ne bawai don basa son su ba a’a suna hakan ne duk wai da sunan jan aji kada a raina su, wasun su kuma a zahiri son su ne basayi amma baza su fahimtar da su hakan ba, a maimakon haka sai su dinga wahalar da samarin nasu suna yaudarar su suna fakewa da wani abu daban don kawai cinma wata manufa ta kashin kansu, sannan bayan sun gama cin moriyar ganga sai su jefar, ma’ana su fito musu a mutum su guje su, babu yaudarar data kai wannan.

Na’am, nasan cewa mace na bukatar kulawa fiye da namiji, dalili kuwa shine ita zuciyar mace ba Kamar ta namiji bace, ita tamkar kwalba ce da takan iya fashewa cikin sauki, saboda haka tana da rauni sosai ba kamar ta maza da zata iya jure abubuwa da daman gaske ba, ita ta mace dole zaka same ta akasarin haka ne. To amma abin dubawa anan shine duka zuciyoyin namu muradin su dayane, wannan muradin ba komai bane face mai kyautata mana, saboda haka idan muka zurfafa tunani to lallai zamu ga ashe dukkan mu ne ke bukatar wannan kulawa ko ince kyautatawa bawai mutum daya ba, a’a saidai daya yafi rinjaye ko kuma in son samu ne duka ya zama daya saboda mutane kowa da irin nashi fahimtar, ba dole ne yanda wannan yake ya kasance shima wancan haka yake ba, don haka nake ganin zai fi armashi idan muka kalla kanmu a matsayin abu daya tunda dama shine zaman tare.

Idan soyayya ta kasance ta rinjaya a bangare daya ne kawai to sai kaga tana ta rawa ta kasa tsayawa daidai yanda ya kamata, wato kamar zata kamar ba zata ba sai ya kasance ta zama matacciyar soyayya domin kuwa ba za a taba jin dadin ta ba, amma yayin da so ya kasance ta kowane bangare akwai kyakkyawar motsi sai soyayyar ta zamo abin sha’awa ga kowa har wasu su gani su dinga kwadayin dama sune, sai soyayyarku ta zama abin kwatance kuma abin koyi ga sauran al’umma, hakan kuma ke sa a cimma babbar muradi wato aure, domin ita ribar soyayya kenan, soyayyar kuwa da duk ta zamo akasin haka to bata cika soyayya ba saidai a kira ta da shashanci da kuma bata lokaci.

So da dama irin wannan matsalar na afkuwa ne tun farko wajen zabin aboki ko abokiyar rayuwa, idan ya kasance mutum baisan wanda ya cancanci yayi rayuwa dashi ba ko kuma wanda kyau, kudi, matsayi ko wani abu daya danganci haka ya makantar dashi ya fada soyayyar wani ko wata to bayan wannan ya shude daga baya sai a dinga samun matsala a tsakani saboda tun farko ba a kulla alakar yanda ta dace ba, an kulla shine sakamakon wani buri da ake so a cimma wanda daga baya kuma ta shude.

Soyayyar gaskiya ba kulla ta ake da wata manufa makamantan wadancan manufofi ba, mutum shi yasan wanda ya ke so ya kuma dace yayi rayuwa tare dashi, sannan ba’a zaban ma mutum aboki ko abokiyar rayuwa shi yasan irin wanda ya ke so amma bazai zama laifi ba idan aka bashi shawara domin komai na bukatar shawara daga iyaye, abokai ko kawaye na gari, domin abokai ko kawaye na gari suke bada shawara ta gari, na banza ko saidai su bada akasin hakan, saboda haka yakamata mu kula da taka tsantsan wajen zabin abokan rayuwa saboda hakan kadai zai bamu damar kyautata musu da basu kyakkyawar kulawa ba tare da nuna gajiya wa ba.

Sannan har ila yau ina mai bada shawara ga ‘yan uwa na maza da mata da mu daina yaudarar juna wajen aikata abinda bami niyya ba don ko a gurin Allah ma babu lada hasali ma saidai zunubi idan akwai cutarwa. Mu kasance mun so juna don Allah da zuciya daya domin babu wata fa’ida idan munyi cuta a tsakanin mu, macuci ko mayaudari bai taba samun nasara ba, bawai ma a soyayya kadai ba a’a a komai ma in zamu duba.

Insha Allah zan takaita a nan na wannan makon don abubuwan nada yawa saidai mu tsakuro wani mu bar wani saboda yanayi amma wanda aka dora shi akan hanya to da sannu zai tafi har inda ake so insha Allah. Da fatan zamu dubi wannan dan takaitaccen bayani da kyakkyawar fahimta mu kuma yi kokari wajen ganin mun gyara.

Daga Dan uwanku mai cike da Kaunarku Sulaiman Umar AC Kaduna

 

Tambayoyin Wannan Mako

Da fari muna so musan sunan ka?

Sunana Adam Ibrahim wanda aka fi sani da Adra

A ganinka/ki wa yafi bukatar kulawa tsakanin mace da namiji?

A gani na mace tafi bukatar kulawa fiye da namiji. Saboda raunin su a halitta ba komai ne suke iya jure wa ba.

Cikin kalma hudu zuwa biyar zaka iya mana bayanin me ake nufi da girman kai a soyayya?

To abinda ake nufi da girman kai a soyayya shine namiji ko mace dayansu ya ringa ji cewa yafi karfin daya. Misali, namiji ya ringa jin yafi mace wayewa ko yafi ta arziki da makamantan su.

Hakan kenan nada Nasaba wajen yankewar alaka?

Kwarai da gaske.

Ta yaya kenan?

Saboda girman kai a soyayya yana haifar da rashin fahimta tsakanin masoya da kuma haddasa rigingimu tsakanin su.

To mun gode

 

 

 

 

Da fari muna so musan sunan ka?

Sunana Zainab Idris amma ana kira na da Zee baby

A ganinka/ki wa yafi bukatar kulawa tsakanin mace da namiji?

A tinani na mace tafi bukatar kulawa akan namiji saboda raunin mu da kuma kunya, mace tafi cancanci kulawa fiye da namiji

Cikin kalma hudu zuwa biyar zaka iya mana bayanin me ake nufi da girman kai a soyayya?

Abinda ake nufi da girman kai a soyayya shine kamar ji-ji da kai, kamar jan aji kenan, amma yana yawa saboda shi daban ne, soyayya kuma bata tafiya da girman kai.

Hakan kenan nada Nasaba wajen yankewar alaka?

Eh sosai yana zama sanadi na yankewar alaka a tsakanin masoya.

Ta yaya kenan?

Saboda in har akwai girman kai ko in ce ji-ji da kai to an dinga samun matsala kenan, kaga kuwa akwai rashin fahimta.

To mun gode

 

Exit mobile version