Connect with us

MANYAN LABARAI

Mace-macen Kano: Gwamnatocin Buhari Da Ganduje Na Jayayya

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahu Umar Ganduje har yanzu ta na kan kujerar na-ki, inda ta ki gamsuwa da rahoton da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhamamdu Buhari ta fitar na cewa, sama da kashi 50 cikin 100 na kusan mutum 1,000 da su ka mutu a watan Afrilu na da alaka da annobar cutar Korona.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce, ya na ja da binciken mace-macen da Gwamnatin Tarayya ta yi, wanda ya nuna cutar Korona ce ta yi ajalin fiye da kashi 50 da a ka samu a jiharsa. An ruwaito Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce, adadin mutane 979 ne su ka mutu cikin makonni biyar a Jihar Kano sakamakon kamuwa da cutar Korona.
Ministan ya yi furucin hakan ne a yayin zaman tattaunawa da kwamitin Fadar Shugaban kasa mai yaki da cutar Korona da a ka gudanar cikin babban birnin kasar na tarayya, Abuja.
Amma rahoton kwamitin yaki da cutar Korona da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa ya ce, kashi 15 cikin 100 na mamatan da su ka mutu ne ya ta’allaka ne sakamakon kamuwa da cutar Korona. Wannan rahoto da fadar gGwamnatin Kano ta fitar a ranar Talata na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan da Ministan Lafiya ya gabatar da rahoton nasa kwamitin na Gwamnatin Tarayya.
Jagoran kwamitin na Jihar Kano, Farfesa Mukhtar Gadanya na asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce, mutum 255 ne kacal a cikin mamata 1,774 su ka rasu sakamakon cutar Korona.
A yayin karbar rahoton binciken da a ka gudanar, Ganduje ya yabi kwazon da kwamitin ya yi, wanda ya ce, ya na kunshe da alkaluma masu gamsarwa da saukin fahimta. Gwamnan ya kara da cewa, shi da kansa zai mika wannan sakamako zuwa Fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin ya kawar da shakkun masu tantama a kai.
Jagoran kwamitin masu bincike na Kano ya ce kashi 70 na mutanen da ajali ya katsewa hanzari sun mutu ne a sakamakon wasu cututtukan kamar hawan jini da ciwon suga. Ya kuma ce kashi 76 cikin mutanen da su ka kwanta dama sun kasance dattawa ’yan shekara 50 zuwa sama. Ya kara da cewa, mutum 1,774 ne su ka rasu daga ranar 1 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2020 a kananan hukumomi takwas da ke kwayar birnin Kano.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: