Sabo Ahmad" />

Mace Mai kamar Maza: Takaitaccen Tarihin Yadda Na Tsinci Kaina A Tukin Tirela -Halima

Mace mai kamar maza, za mu so ki bayyana mana kanki. Sunana Halima Alhassan, kuma ina daya daga cikin direbobin kamfanin Dangote, masu zirga-girga da kuma safarar kayayyakin kamfanin zuwa sassan daban-daban na wannan kasa, har ma da kasashen waje. Ni ‘yar garin Ubajina ce da je Lokaja shalkwatan jihar Kogi, shekaru na 36. Ga shi kina cikin sana’a irin ta maza, mene ne sanadiyyar shigarki cikin irin wannan sana’ar ta tukin babban mota kuma Tirela?

Sanadiyyar shiga ta cikin wannan sana’ar na tuki shi ne, ni ina Ubajina a Lakwaja wata rana sai ga Hajiya Rabi’atu Abubakar ‘yar jihar Katsina ce ta zo ta ce min za a ba ta mota. Na tambayeta me ta ce? Ta ce min mota za a ba ta, na sake tambayarta cewar mota za ki tuka ta ce min eh. Nan take ni ma na kudiri aniyar cewar, ni ma matukar matar nan ta tuka mota, to ni ma sai na tuka. Haka na bayyana wa jama’a na kuma sha musu alwashi, na ce matukar Hajiya Rabi ta ja mota to ni ma zan ja ta. Ana haka kawai san na ga ta hau mota ta kuma ja ta, na ce aahh! To, tun da yanzu mata har suna da zuciyar tuka mota, mene ne ya sa, ni ma ba zan shiga cikin wannan sana’ar ba? Daga nan na kwallafa wannan lamarin a cikin raina, nan take na kira kanin mahaifina (domin mahaifina Allah ya yi masa rasuwa) na ce masa Baba ga fa wani sabon abu da na ga mata yanzu sun runguma suna sana’ar tuki tirela, ni ma ina son na tuka.

A karon farko kamar ma ya ji haushin maganar ne sai ya kashe wayarsa, ban gajiya ba na sake kiransa na sake yi masa magana, sai a lokacin ya ke ce min na bari sai ya yi tunani, bayan da ya yi tunaninsa sai ya ce min to Allah ya sa hakan shi ne ma fi alkairi, tun da ya ga na nace na dage kan wannan bukatar tawa. Nan sai ya gargade ni ya ce na yi kokarin kare mutunci na, na tsaya na yi aikin da ke gaba na tsakani da Allah na kula sosai, na ce masa babu damuwa zan yi hakan. Daga nan meye kuma ya faru? Bayan mun gama haka, sai na zo na shiga sha’anin na fara ne da gwaji, ina ta koyo, na zo na bi mota yaron mota kenan wanda ake cewa (Karen Mota) domin na ga yanayin abubuwan da kuma tsayuwa sosai domin lura da komai yadda ya dace, daga baya kuma Allah ya taimakeni na iya na zo na fara jan mota da kaina.

Shi wannan horon da kika samun, kin samu ne a karkashin maza ko matan sannan kuma a ina ne kika samu horon har kika goge? Na samu horon nan ne a karin Ubajina a wajen wani shugaban direbobi na kamfanin Dangote wadda ke shugabntan wan rukuni na ‘(FLEET 3)’ wato Alhaji Isiyaku Faksari shi ne ya koya min mota na kuma iya. A lokacin da ya koya min mota, su manya ne ba a barinsu su tuka mota ko su yi loda ma gaba daya tun da su ne shuwagabanin direbobinmu, amma sai kamfani ta ce mishi ya koya min sosai, a dalilina ni kadai ya sake daukan mota ya ke bin hanya domin ya tabbatar na iya mota na kuma goge domin hakn ne ya yi tsayuwar daka wajen ba ni horo kan tuki. Domin ni da na tashi neman koyon mota na je kai tsaye ne na samu shugaban direbobinmu, sai ya ce min shi Alhaji Isiyaku Faskari shi ne zai koya min mota cikin kwanciyar hankali ba tare da wani matsala ba. to da muka je muka fara hawa titi da shi muna lodin kayyakin kamfani, a lokacin da muka fara lodi mun tafi wani gari ne wai Gaidam, Unguwa Uku a Jihar Kano abun da ya faru da mu ba zan taba mancewa da mutumin nan a rayuwa ta ba, dalilin da ya sa kuwa ba zai taba mancewa da wannan bawan Allah ba a wannan garin ne ya fara bani mota na ja da kaina.

Lokacin da ya bani, da na hau kan kujerar mulki na direba na zauna ‘SIT’ da ya ga yadda na rike matokin mota (siteri) sai ya ce tabbas daga ganin yadda na iya zama a motar nan ba zan ba shi wuya wajen koyon mota ba. cikin yardar Allah da ikonsa kafin wata biyar na iya mota tsaf, abun da ya ja ni sosai har na kai wata wata tara shi ne tuki da baya ko kuma shan kwana (ribas), ka san a tukin mota Ribas shi ne babbar abu mai wuya, wannan dalilin ne ya sa na kai wata tara daga wannan lokacin kuma hanuna ya mike da tukin mota babbar mota, nan take kuwa aka bani babbar mota Tankan a fara ja, yanda na kware a mota sai kuma gashi na zama abun kallo da ban mamaki ga jama’a a kowani lokaci, samman idan jama’a suka ga na yi yo lodin manyan kaya shake da mota kuma su ga ina janta a cikin kowani yanayi, wannan dalilin ne ya sa jama’a suke ganin abun mamaki a gareni. Ya maganar aure tun da kin kama sana’ar tuki jama’a za su su ji wannan amsar daga bakinki. Kina da aure, in kina da aure ya kike tafiyar da rayuwar auren tun da sana’arku ta tafiye-tafiye ce? Allah ya yi wa mijina rayuwa, amma ina da ‘ya’ya, kuma dai hakan na ke kula da su, kula kuwa sosai wadda wani mai uban ma bai yi musu, ina bai wa ‘ya’yana kulawa duk da ina wannan sana’ar ta tuki sosai.

To, ta yaya ‘ya’yanki suka amshi wannan sana’ar taki da kuma yadda suke kallonki a cikin wannan sana’ar taki? Gaskiya ni dai yarana suna ba ni hadin kai sosai kuma suna kokari sosai wajen karfafa min gwiwa kan dagewa a bisa sana’ata, kuma gaskiya ina kula dasu ta wannan sana’ar sosai. Zan iya tunawa wata rana ma wasu ‘yan jarida sun zo domin yin hira da wasu daga cikin ‘ya’yana Nafisa da Dayyiba, a lokacin da ‘yan jaridar nan suke hira da su, sai ita Nafisa take bayyana musu cewar kamar ni bana ma son su san Babansu ya rasu, saboda ko mai Uba a duniya ba zai nuna musu komai ba, ba zai nuna musu kulawa ba, domin ina kula da su sosai ta wannan sana’ar. Gaskiya ni Allah ya taimakeni sosai a kan ‘ya’yana. Daga cikin ‘ya’yana na farko na yi mata aure da wannan sana’ar, na biyu kuma tana nan ta zama wata abu, na ukun kuma ina sa ran in ta kammala sakandari zan sanyata a bangaren Injiyarin a sashin fasafar zamni da yardar Allah. Kasantuwar aikinku akwai hada-hada, ya yanayin mu’amalarku da sauran abokan aiki maza ke nan? Ka san wannan aikin, aikin maza ne, kuma na zirga-girga ne sosai muna ganin abubuwa sosai iri-iri, amma dole ne kawai za mu yi hakuri tun da mun zo mun shiga aikin da ba namu ba, dole ne mu tsaya tsam mu ga yadda ake abubuwa domin mu ma mu daura don yin daidai din.

Wadanne kalubale kike fuskanta kasantuwarki mace mai tuka babbar mota Tirela? Gaskiya a matsayina na mace akwai direbobi da yawa da su kan zo min da wasu abubuwan da basu dace ba, amma da yake na san mene ne na ke yi kuma mene ne hadafina ina kokarin kawar da kaina daga dukkanin wasu ababen da ka iya zubar min da mutunci, kai akwai wanda ya taba zuwa min ma gaba-da-gaba, amma irin wannan masu furta ababen banza suna da yawa, sai dai Allah ya kare, kuma dole ne mu yi ta hakuri da hakan. Akwai kiran da za ki wa mata ‘yan uwanki mata dangane da tashi tsaye domin neman na kai, kasantuwar wasu abubuwan mata sukan ce wannan ai na maza ne zalla bai kamata mata su shiga yin saba. Malam! gaskiya ni ina da kira ma sosai, wannan kiran nawa ba kawai wa mata ne na ke yi ba; kai tsaye ina da kira ne zuwa ga gwamnatin tarayya, ina kira ga gwamnatin tarayya ta karfafi mata kan neman na kai, idan za su karfafi mata to tabbas za a samu mata suna shiga ana damawa da su, domin mace tana da zuciyan da in tace za ta yi abu to tabbas za ta yi, saboda mu yanzu ka ga a kamfaninmu shi ma Dangote ya fi alfahari da mu mata, saboda bamu yawan yin ganganci a hanya, bamu yawan hatsari, bamu cika jawo masa hasara ba.

Akwai aiyuka birjik da in aka bude domin koyar da mata da dama za mu koya kuma za su tsayu da kafafunsu wajen yi, ni yanzu ina da burin koyon mota irin Buldoza din nan da kuma irin su Katafila duk ina son na koya, don haka irin wadannan koyon bayan za a samu mata da dama da za su shiga cikin sha’anin manyan sana’o’i wadda hakan zai taimaka sosai wajen dauke musu dawainiyarsu. Domin akwai mata da daman gaske da suke son su ke neman na kansu ko shiga irin sana’o’i irin wannan amma suna ganin kamar ba za su iya ba, ko kuma basu da damar yi, ko ni kafin na zo na fara ai na wahala, idan na ce maka zan baka labarin yadda na sha wuya a wannan sana’ar wallahi za ka yi kwalla domin wata rana na kan wayi gari ko naira biyar bana da shi, kai kudin da zan sanya a waya na kira yara na ji halin da suke ciki babu a wani lokaci, sai dai mahaifinyata da ta yi ta taimakamin yanzu ga shi komai ya zama tarihi ya wuce, don haka tsayuwa a zauna waje guda ba namu bane, yanzu lokaci ne na ki tashi ke nema.

Don haka ina kiran gwamnati don Allah ta samar da wasu tsare-tsare zallarsu kawai don mata ne wadanda zai baiwa mata damar shiga su nemi yadda za su yi da rayuwarsu. Ga ‘yan uwana ma ta kuma tabbas mu ci gaba da buga-bugar neman sana’a domin yanzu lokacin zama waje guda fa ya wuce, wani abun muddin baki tashi ba, ba zai iyu miki ba, ko kuma ki zauna kina ganin wahalar iyuwar wani abun duk bai kamata ba, tashi tsaye domin nem shi ne a gabanmu. Yanzu ni da na ga Hajiya Rabi tana tuki nima na ji sha’awa na kama ba gashi na iya ba, yanzu babu wani wajen da wani direban kamfaninmu zai yi lodi ya kai wadda ni mace ba zan iya ba, ka ga wannan na rigaya na cire wa raina cewar na miji ne kadai zan iya ga shi na iyan kuma. Yanzu ke kina lodi daga Ubajana, Lokaja zuwa ina da ina a Nijeriya?

Yanzu haka wannan kayan da ka gani da shi ma na yi lodinsa ina hanya ne zai tafi Madagali shi ne ka tsaida ni kake min wannan tambayoyin. Ni da ka ganni babu inda ba a zuba min kaya kuma a ja na kai cikin kwanciyar hankali, muna zuwa har zuwa su kasar Nijer, su Yenaguwa da Oyo kai ko’ina ina zuwa na kai kayan kamfanin Dangote.

Exit mobile version