Hajiya Hauwa’u Ibrahin Zariya, ita ce shugabar mata masu noman albasa ta Jihar Kaduna. Wakilinmu Idris Umar ya ziyarci ofishinta inda ya zanta da ita kan abubuwan da suka shafi mata da dama. Ga tattaunawar kamar haka:
Hajiya Hauwa’u za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu. Assalamu alaikum warahmatullah, sunana Hauwa’u Ibrahim, Zariya kuma an haifeni a Tukur-Tukur Zariya, na yi makarantar firamare a Tsoho Abdullahi LGA da ke Tukur-Tukur. Na yi sakandare a Jama’atu Nasril Islam a Kofar Kibo, bayan na gama Junior, sai na je Abdurrahman Gora Tudun Zariya, a nan ne na karashe karatun sakandire dina. Daga baya sai na je FCE na karanta Arabic/Hausa, yanzu kuma in sha Allah ba da dadewa b azan ci gaba da karatun B.Ed.
Hajiya mene ne dangantakarki da noman albasa a Jihar Kaduna? Dangantakata da noman albasa a Jihar Kaduna shi ne, ni ce shugaban mata a kungiyar manoman albasa da masu sarrafata ta Jihar Kaduna.
Ko za ki gaya wa duniya abin da ya ba ki sha’awar shiga harkar noman albasar a matsayinki na ‘ya mace? Sosai kuwa, na farko shi ne na taso a gidan manoma albasar. Na biyu ni mace ce mai son neman abun kanta don ina tausaya wa mata bisa mawuyacin halin da suke fadawa a bangaren harkokin yau da kullum. Saboda haka ne na yi shawara da maigidana da ya bani damar shiga cikin harkar noma kuma ya amince min ga shi cikin ikon Allah komi na tafiya yadda ake bukatarsa.
A zuwa yanzu wasu irin nasarori ne kuka samu a cikin harkokin noman albasa? Lallai muna samu alherai da dama a cikin karakar noma da kasuwancin albasa da muke yi. Mun samu rufin asiri sosai wanda muke kara yi wa Allah godiya, don a cikinsa muke bai wa maigida taimakon kudin makarantar yara, sannan muke samun daukar dauyin yara mata yayin zuwansu gidan aure.
Ta ya ya kike gudanar da wannan sana’ar a matsayinki ta ‘ya mace kuma matar aure? Gaskiya lamarin akwai wahala, sai dai ni na sami gudummawa sosai wajen maigidana, Malam Abdul-Kadir, domin shi ne ya koyamin hulda na manonan ya kuma wayarmin da kai wajen yin mu’amula da manoma da ‘yan kasuwa ta yadda make saye da sayarwa. Bisa hakane nake jinjina wa mijina, domin idan mace ba ta sami wayayyen miji ba, to noma ba zai yi wu a gare ta ba.
To da ina da ina kuke kai albasar taku? Babu inda kasuwa ba ta kai mutum, amma mun fi bayar da karfi a bagaren Legas, Fatakwal da sauran jihohin Kudu. Wani irin kalubale kuke fuskanta yayin da kuke gudanar da kasuwanciku? Lallai mukan samu kalubale da yawa, dan kana iya sayan albasa ka tura ta Kudu bayan an kai albasar sai a fadi, ko ta lalace ko kuma yana iya yiwuwa ka sai albasan a Kudu kadan, amma in an je a sami kasuwa ta yi kyau sai a samu alheri mai yawa, ana iya samun nasara kuma ana iya samun faduwa.
Haka dai muke gudanar da kasuwancinmu wata rana a fadi wata rana a tashi Wace shawara za ki bai wa matan da suke ganin noma ga ‘ya mace kauyanci ne? Gaskiya akwai shawara masu amfani, na farko zance mata ku bude kunni ku ji sosai, mace mai sana’a ta fi farin jini a wajen mijinta. Na biyu kuma, yaran mace mai sana’a da ban suke a cikin anguwa. Mace mai sana’a ta fita daban a wajen taron biki har a makarantar Islamiya balle a wajen dangin miji. Don haka shawarata ga mata ku roki mazajenku dama ku fito don mu yi sana’ar da za mu taimake su a bangaren rayuwar yau da kullum.
Wani sako kike da shi ga shugabaninki wadanda suka baki wannan dama? Gaskiya akwai mataimakin shugabanmu na kasa baki daya, Alhaji Dakta Isma’al Dan Nuhu Jibiya, ina mashi fatan alheri da shuganmu na jiha, Alhaji Muhammad Kargi shi ma muna mika godiyarmu gare shi. Kuma ina mika godiya ga ‘ya’yan kunyiyar manoman albasa da sarrafata na kasa baki daya duk ina masu fatan alheri.
Ko akwai wani abu da kike so ki ce da ba a baki damar fada ba? Eh, akwai ina kira ga gwamnati jiha da ta tarayya da su tallafa wa kungiyar manoman albasa bisa irin kyawawan tsarinsu da kokarinsu na kawo ci gaba a kasa baki daya