A cikin makon da ya gabata ne, Sarkin yankin Tilden Fulani, da ke gudumar Toro a Jihar Bauchi, ya yi karin nadin mutanen da zai yi aiki da su a masarautarsa, don samun ci gaban al’ummar yankin, da na karamar hukumar da ma jihar Bauci baki daya. Daga cikin wadanda aka nadan akwai zinariya. Jim kadan, bayan kammala nadin nata, wakilimmu da ke Jos LAWAL UMAR TILDE, ya tattauna da ita. Ga kuma yadda hirar tasu ta kasance
Masu karatunmu za so ki gabatar da kanki gare su, don su san tare da za mu tattauna a halin yanzu ? Sunana Hajiya Hadiza Gazali Kasimu, an haife ni a garin Jos, shekara ta 1960. Na fara yin karatun addini daga nan na ci gar da makarantar boko. Na yi firamare daga aji daya zuwa bakwai, daga nan na samu tafiya sakandare da ake kira Sardauna Memorial School a Titin Zariya Jos.
Bayan na gama a shekara ta 1980, sai na wuce School for Basic Studies Ahmadu Bello da ke Zariya. A nan na samu kammala karatun Digiri dina a 1983. Daga nan, sai na samu zuwa hidimar kasa a Legas. Na fara aikin hidimar kasa a hukumar NITEL, amma daga baya na nemi a sauya mini gurin aiki zuwa Babban Bankin Nijeriya, Allah kuma ya taimake ni, na yi hidimar kasa. Ina gama aikin hidimar kasar, sai suka dauke ni aiki, wanda na ci gaba da yi har na kai matsayin Darakta, kafin suka yi mini ritaya a 2018
Bayan kin yi ritaya, yanzu wace harka kike yi? Kafin ma in yi ritaya, na fara noma, ina da gonaki a Tilden Fulani, cikin karamar hukumar Toro a jihar Bauci da wadansu a yankin Jingir, kan iyakar jihar Filato da Kaduna, kuma na hada da kasuwanci, ina da kamfani da ake kira KUBURA-VENTURE NIGERIA LIMITED Abajuba, inda nake gudanar da hakokin kasuwanci da suka shafi kayan gwal, wato Zinariya kuma muna aikin ilimantarwa, inda nake ilimantar da mutane a kan hada-hadar kudade da bankuna ba tare da sun cutu ba, wanda kuma suna da wadansu korafe-korafe, su kan kawo mana kukansu mu bincika mu duba, mu ba su shawara. Haka kuma muna taimakon matan da muka gani suna da hazaka, don su bunkasa sana’o’in da suke yi a cikin gidajensu da wadanda muka gani suna da fasahar gudanar da wadansu sana’o’i, na daban. Harkar aikin gona din ma, ina yi, sai dai ban ba shi mahimmanci ba, saboda matsalar rashin tsaro da yanzu kasar ke fuskanta.
Kin taba rike wani mukami na wata kungiya, kafin a ba ki wannan mukami na Zinariya?
Na taba rike mukamin Assistan Secretary Cibiyar Institue of Directors Abuja Zone, yanzu kuma ni mamba ce a irin wadannan kungiyoyi na ‘professional budies’ a cikin kasar nan. Muna ilimantar da mutane da ba su shawarawari a kan harkokin da suka shafi sana’o’insu da kasuwancinsu don su samu cim ma nasarar bunkasa su.
Ganin irin gudummowar da kike bayarwa wajen ci gaban al’umma, mai girba Sarkin yankin Tilden Fulani, ya ba ki mukamin Zinariyan Tilde. Ya kika ji, kuma me za ki ce? Zan ce Alhamdu Lillahi, na yi murna kwarai, da Allah ya zabe ni a cikin mutanen da aka ba su makami a wannan masarauta, kuma ina gode wa sarki da ya ga na dace ya ba ni wannan mukami. Idan muka koma kan harkokin da suka shafi al’ummar kasar nan a daidai wannan lokaci da muke tattaunawa, shugaban kasa da gwamnonin jihohi sai jawabai suke wa mutanen kasar nan game da kudaden da za su kashe a wannan shekara ta 2022, wane kira ko shawara kike da shi game da kasafin kudin?
Kira ko rokon da nake da shi zuwa gare su shi ne su ji tsoron Allah, su yi ta aiwatar da kasafin kudin kamar yadda suka yi wa al’umma bayani, domin sau da yawa za ka ji an ware kudi za a yi aikin kaza, amma daga baya a nemi aikin a rasa, gaskiya talakawa har yanzu ba su gani a kasa ba. Ina fata cikin ‘yan watannin da suka rage wa shugaban kasa da gwamnoninsa na wa’adin cikar mulkinsu za su yi wani abu da za su bar kyakkyawar tarihi ga al’ummar kasar wanda za su rika tunawa da su, domin Allah ya albarkaci kasar nan da duk irin nau’i, na arziki da duk wata kasa ta duniyar nan ke tinkaro da shi, ga mu da al’umma masu hazaka, ga kasar noma.
To mecece mafita? Mafita a nan uta ce, shugaban kasa da kansa zai rika sa ido a kan kowane tsari aka kaddamar da shi, kuma ya tabbatar da an aiwatar da shi daidai ba wani almundahal.
Game da matsalar rashin tsaro, wadda a baya kika bayyana cewa, yana daga abin da ya hana ki ba da karfi a kan aikin gona, wace shawara za ki bayar musamman a jihohimmu na Arewa?