Yusuf Shuaibu" />

Mace Ta Kone Ciki Da Gwiwar ‘Yar Aikin Gidanta Saboda Naira 500

Wata mata mai suna Misis Mariam Hafia, ta kone ciki da kwiwar ‘yar aikin gidanta mai suna Mansura da dutsan guga na lantarki. Ita dai Mansura ta na aiki ne a gidan mijin Hafia da ke kan titin Ola Akinpelu cikin yankin Alimosho ta Jihar Legas, inda a ka bayyana cewa, ma’auratan sun dauko wannan yarinyar ne tun daga hannun iyayenta da ke Jihar Oyo.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, Hafia ta bai wa Mansura kudi naira 1,500 ta ijiye mata a ranar 29 ga watan Satumba, amma sai yarinyar da kawo mata naira 1,000 lokacin da ta tambaye ta. Hafia ya ta zargi Mansura da kashe mata naira 500, inda ta yi amfani da dutsen guga mai zafi wajen kona mata ciki da gwiwa.

Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, matan ta ki kai Mansura asibiti domin a yi mata maganin ciwon da ta ji mata.

Wani makwabcinsu wanda ya samu labarin lamarin ya kai wa gidauniyar kare hakkin yara mai suna Esther Child Rights Foundation rahoton lamarin, inda daga nan ne su ka kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda da ke yankin Mosalasi.

Wata ma’aikacin wannan gidauniya mai suna Misis Chinyere Tony, ita ce ta ceci Mansura, inda ta bayyana cewa, yarinyar ta yi amfani da naira 500 wajen sayan lattafi a makaranta. Tony ta bayyana cewa, “wani mutum ya kai rahoton lamarin a ofishinmu ranar 8 ga watan Oktoba, inda mu ka samu nasarar ceto yarinyar a washagarin ranar. Mun gano cewa, matan ta yi amfani da dutsen guga wajen hukunta yarinyar, saboda ta yi amfani da kudinta naira 500 wajen sayan littafi. Yarinyar ta bayyana cewa, ita daya ce wacce ba a sayen mata littafi ba a ajinsu. “Matar ta kone cikin da gwiwar yarinyar da dutsen guga, inda ta ke ikirarin cewa, yarinyar ta fada kan dutsen guga ne lokacin da ta ke guge wasu kaya.”

An bayyana cewa, ‘yar sanda sun damke matar, amma daga baya sun sake ta bisa umurnin da DPO ya ba su, sannan su ka mika mata wannan yarinya.

Gidauniyar ta kara kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke da makwabtaka da yankin Isokoko, inda su ka bayar da rahoton DPO na sakin Hafia. Shugabar wannan gidauniya mai suna Misis Esther Ogwu, ta bayyana cewa, sun rubuta korafinsu ga ma’aikatar shari’a ta Jihar Legas da kuma hukumar da ke yaki da safarar yara kanana. Ta ce, “a cewar yarinyar, Hafia ta ba ta kudi na naira 1,500 na ijiye mata, lokacin da ta bukaci ta ba ta kudin, sai ta kawo mata naira 1,000. Abin takaici ne a ce irin wannan ya na faruwa a cikin al’ummanmu. Abin da ya fi takaici shi ne, yadda ‘yan sanda su ka yi watsi da lamarin. Tun da farko dai, an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda da ke yankin Moshalashi, inda a ka gayyaci matar da zo ta yi bayani. Kafin wannan lokacin dai, matar da yi wa yarinyar barazanar idan ta kuskura ta fadi hainihin abinda ya faru, to za ta daina biyan mata kudin makaranta. “An gabatar da yarinyar tare da matar domin su yi bayani. Yarinyar ta zorata, inda ta bayyana cewa, ta fado ne a kan dutsen guga, wanda kuma ba haka ba ne. DPO ya bayyana mana cewa, babu isasshen shaida da zai sa a gurganar da matar a gaban kuliya. Mun dauki matakin rubuta korafi ga ma’aikatar shari’a ta jihar da kuma hukumar da ke yaki da safarar yara kanana.”

An kara kai rahoton lamarin ga sashen hukumar da ke kare hakkin Dan’adam, a yankin Alagbon, inda a ka damke Hafia. Shugabar sashen na hukumar ACP Mary Ajunwa ta bayyana cewa, a halin yanzu ana gudanar da binciken a kan lamarin, sannan kuma an samu nasara cafke matar. Ta ce, “an mika yarinyar ga iyayenta da ke Jihar Oyo, inda ba sa son jami’an tsaro su ga raunin da yarinyar ta samu. Na yi amfani da ofishina inda na bayar da umurnin a dawo da yarinyar zuwa Jihar Legas, kuma an samu nasarar dawo da yarinyar. Muna kokarin sanin ainihin abinda ya faru. An damke wacce a ke zargi, inda a halin yanzu ta na hannun jami’an tsaro. Mun ga raunin da ta yi wa yarinyar, sannan mu na kokarin sanin dalilin da ta yi hakan. Matar ta na ikirarin cewa, yarinyar da fado ne a kan dutsen guga. Amma idan a ka kalli raunin, ba ma tunanin cewa yarinyar ta fado ne a kan dutsen guga. Mun tabbatar akwai wani abinda matar ba ta son fada mana.”

Daraktar ma’aikatar shari’a ta Jihar Legas, Misis Olayinka Adeyemi, ta bayyana cewa, nan ta ke hukumarta ta dauki matakin gaggawa lokacin da gidauniyar da rubuta mata korafinta, amma sai a ka samu sakaci daga wajen DPO wanda a ka kai masa rahoton lamarin. Ta ce, “ban taba ganin irin wannan azabtar da yarinya ba, inda kuma matar da ke ikirarin cewa yarinyar da fado ne a kan dutsen guga. Ta yayi za a ce yarinya ta fado a kan dutsen guga kuma har ta samu irin wannan raunin? Idan da gaske ne ta fadi a kan dutsen guga ne, to za a samu shaidar dutsen guga a jikinta. “Yarinyar ta samu mummunan raunin kona a wurare guda biyu a jikinta. Wannan ba karamin abin takaici ba ne. mun gano cewa, ofishin ‘yan sanda guda biyu da a ka fara kai rahoton lamarin sun amshi na goro. Inda su ka bayyana cewa, yarinyar ta fadi ne a kan dutsen guga, sannan su ka saki wacce a ke zargi.”

Adeyemi ta cigaba da bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta cigaba da binciken wannan lamarin har sai an tabbatar da yin adalci. Ta kara da cewa, za a kula da Mansura har sai ta warke. Ta ce, “mun samu labarin cewa, matar ta dauko wannan yarinya ne tun daga gidan iyayenta domin ta yi aiki a gidan. Iyayenta su na kokarin rufe lamarin, sakamakon sun samu labarin hukumomi sun shiga cikin maganar, sannan kuma su ne su ka kai yarinyar zuwa Jihar Legas. “Abinda mu ka shirya a halin yanzu dai shi ne, mun amshe yarinyar daga hannunsu domin yi mata jinya, yayin da ‘yan sanda su ke gudanar da bincike a kan lamarin. Ba mu so yarinyar ta bar Jihar Legas, saboda an aikata wannan laifi ne a Jihar Legas.”

Exit mobile version