Mace Ta Sayar Da Jaririnta, Ta Ce Wa Mijinta Ya Mutu

Rundunar ‘yan sandar Jihar Imo, ta damke wata mata mai suna Chinaza Ukaonu tare da wasu ma’aikatan asiriti guda biyu, bisa zargin su da sayar da jariri. Kakakin rundunar ‘yar sandar Jihar Imo, Orlando Ikeokwu, shi ya tabbatar da hakan a garin Owerri. Ya bayyana cewa, an damke matar ne sakamakon rahoton da mijinta mai suna Promise Ukaonu, ya kai karar matarsa a ofishin ‘yar sanda, inda ya ke zargin matarsa a kan ta yi masa karya game da dansa.

Damke Misis Ukaonu, ya kai ga cafke wacce ta sayi jaririn mai suna Amadi Chioma. Sannan ta kai ga kame wasu mata guda biyu ma’aikatan asibiti, wadanda su ke kulawa da Misis Ukaonu tun daga lokacin da ta dauki cikin masu suna Esomonu Dorathy da kuma Eke Catherine. ‘Yan sanda sun bayyana wa manema labarai cewa, an samu nasarar kwato jaririn.

Da ya ke bayyana yadda ‘yan sanda su ka damke wadanda a ke zargin, kakakin rundunar ‘yan sanda ya ce, “a ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2019, tawagar ‘yan sanda su ka damke Chinaza Ukaonu, Amadi Chioma, Esomonu Dorathy, Eke Catherine dukkan su mata ne, bisa bayanai sirri da ‘yan sanda su ka samu. “Chinaza Ukaonu ta bar gida tare da tsohon ciki dan wata takwas da niyyar za ta je wurin ‘yar’uwarta wacce ta ke zaune a garin Ubomiri cikin karamar hukumar Mbaitoli, inda ta tafi haihuwa a wurinta. Lokacin da mijinta mai suna Promise Ukaonu ya gudanar da bincike, sai ya gane cewa ba ta gidan.

“Bayan wasu ‘yar watanni, sai ya samu kiran wayar salula cewa matarsa ta haihu amma dan bai zo da rai ba. Lokacin da ya bukaci ya ga gawar jaririn, sai matarsa ta fada masa cewa, ta nannade shi a makin leda sannan ta jefar da shi. Shi dai bai gamsu da wannan labara ba, inda ya kai lamarin ga ofishin ‘yan sanda, inda ta kai ga damke Chinaza Ukaonu, wacce ta amsa cewa ta sayar wa Amadi Chioma da jaririn kan kudi naira 500,000 tare da taimakon wasu ma’aikatan asibitin guda biyu masu suna Esomonu Dorathy da kuma Eke Catherine, wadanda su ka taimaka mata har zuwa lokacin da ta haifu. “An samu nasarar kwato jaririn, sannan ana gudanar da bincike a kan lamarin.

Exit mobile version