Bibiana Steinhausce mace ta farko da ta fara alkalancin wasa a kasar Jamus kuma itace mace ta farko wadda ta fara alkalancin wasa a manyan gasannin a nahiyar turai da suka hada da Firimiya ta kasar ingila, Laliga ta kasar sifaniya,Siriya a ta kasar Italiya sai kuma gasar League 1 ta kasar faransa.
Bibiana wadda kuma ‘yar sanda ce, mai shekaru 38 tayi alkalancin wasan da aka fafata ranar Lahadi tsakanin kungiyoyin Hertha Berlin da Werder Bremen. Wasan da aka fafata a katafaren filin wasa na Olympic na birnin Berlin.
Bibiana ta taba alkalancin wasan karshe na zakarun turai na mata na wannan shekarar sannan kuma tana yin alkalancin wasa a gasar rukuni na biyu na kasar jamus.
Ta ce ta yi farin ciki sosai da wannan dama da aka bata a kasar Jamus, kuma ba zata taba mantawa da wannan ranar ba,inda tace babban farin cikin shine itace mace ta farko mai gashi wadda tayi alkalancin wasa a tarihin manyan gasannin a nahiyar turai.