Connect with us

LABARAI

Mace ‘Yar Jam’iyyar ADC Ta Shiga Takarar Kujerar Gwamnan Bauchi

Published

on

Mace mai neman kujerar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Baheejah Mahmood ta tsunduma cikin jam’iyyar ‘Adbance Congress for Democracy’ ACD, domin ci gaba da yakin neman kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2019 da ke tafe.
Baheejah wacce ta amshi katin shaidar kasancewa mambar jam’iyyar a mazabarta da ke Nassarawa B da ke Azare a karamar hukumar Katagum da ke jihar ta Bauchi.
Da take bayani wa magoya bayanta bayan amsar katin shaidar kasancewa ‘yar jam’iyyar a jiya Lahadi, Baheejah ta sha alwashin cewar jam’iyyarsu ta ACD ita ce za ta lashe kujerar gwamna a jihar Bauchi.
Ta ce, ta shiga neman kujerar gwamnan jihar Bauchi domin burin da take da shi na daukaka darajar tattalin arzikin jihar, tallafa wa talakawa, da kuma shawo kan matsalolin da suka yi wa jihar ta Bauchi katutu, inda ta sha alwashin cewar da zarar ta tsunduma kafarta a jihar kakar ‘yan jihar ta yanke kasa domin za ta yi maganin matsalolin da suke akwai.
Baheejah ta ce; “Matsalolin da matasa, mata, marayu da marasa galihu suke da shi, inda hanyoyin kawo karshensu domin na gama karantar matsalolin da kuma kalubalen da suke jibge don haka ina da hanyoyin fitar da jihar daga matsalar ci gaban tattalin arziki,”
“Masu ruwa da tsaki a jihar da suka kunshi matasa, dattawa, mata sun bukaci na fito na nemi kujerar gwamna a bisa yakinin da suke da shi na zan gyara musu matsalolin da suke addabarsu, a bisa yakininsu na ni zan ceto jihar nan ina mai shaida musu cewar na fito kuma da yardar Allah zan samu gagarumar nasarar lashe kujerar jihar Bauchi domin cetota,” Inji ta
‘Yar takarar ta bukaci jama’an jihar Bauchi da su hada karfi da karfe wuri guda domin mara mata baya kan yunkurinta na ceto jihar daga rugujewar tattalin arziki, rashin aikin yi, talauci, daidaita tsara lamura, tabbatar da jin dadi da walwalar jama’an jihar.
Ta yi fatan jama’an jihar za su rungumi manufarta hanu biyu biyu domin ta kai ga shiga gidan gwamnatin jihar, wanda hakan in ya faru zai sauya tarihin jihar na samun mace ta farko a matsayin gwamnan jihar.
Darakta Janar na yakin neman zabenta, El- Faruk Gado ya Shaida cewar jam’iyyar ACD tana da muradin shawo kan matsalolin da suke jibge a Nijeriya, don haka ne ya nemi jama’a su runguni ACD domin fidda Nijeriya daga halin da take a yau.
ElFaruk ya bayyana cewar an shiga wani yanayin da ake neman nagartattun shugabinni a kasar nan don haka ya shaida cewar Baheejah tana da nagartar da zata kyautata shugabanci yana mai kiran a zabeta.
Ya kara da cewa sun zo da muhimman tsare-tsaren da ya su aiwatar domin kawo ci gaba mai daurewa a jihar ta Bauchi.
Shugaban jam’iyyar ACD a karamar hukumar Katagum, Alhaji Adamu Nasiru ya gode wa Baheejah a bisa shigo wa cikin jam’iyyar inda ya yi bayanin cewa wannan matakin zai bata zarafin kada kowani dan takarar gwamna a jihar.

Advertisement

labarai