Mace Za Ta Iya Bai Wa Mijinta Zakka?
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mace Za Ta Iya Bai Wa Mijinta Zakka?

byDakta Jamil Zarewa
2 years ago
Zakka

Assalamu alaikum. Malam Mene ne sahihi a kan mace ta ba wa mijnta zakkah?

Wa alaikum assalam, ya halatta a zancen mafi yawan malamai saboda hadisin Zainab matar Abdullahi Dan Mas’ud wanda Bukhari ya rawaito a sahihinsa a lamba ta: (1462) da kuma Muslim a hadisi mai lamba ta: (1000) lokacin da ta nemi fat’wa a kan ba wa mijinta sadaka kuma Annabi (SAW) ya halatta mata hakan.

Malaman sun kafa hujja da wannan hadisin saboda kalmar sadaka ta kunshi farilla da sunna.

Aya ta (60) a suratu Attaubah ta yi bayanin nau’o’i takwas na mutanen da ake bawa zakka, daga ciki akwai talaka, hakan sai ya nuna mutukar miji talaka ne matarsa za ta iya ba shi zakka, tun da ba a samu dalilin da ya fitar da shi ba.

Sai dai Ibnul Munzir ya hakaito ijma’i cewa: “Bai halatta miji ya ba wa matarsa zakka ba idan tana fama da talauci, tun da zai iya wadata ta, ta hanyar ciyarwar da Allah ya wajabta masa.

Don neman karin bayani, duba: Sharhul Mumti’i (6/168) da kuma Fataawa Allajnah Adda’imah (10/62)

Allah ne mafi sani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1
Bakon Marubuci

SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1

February 28, 2025
Idan Mace Ta Yi Barin Cikin Wata Biyu, Za Ta Dakatar Da Yin Sallah?
Fatawa

Idan Mace Ta Yi Barin Cikin Wata Biyu, Za Ta Dakatar Da Yin Sallah?

May 5, 2024
Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta
Bakon Marubuci

Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta

April 10, 2024
Next Post
UNEP

Babbar Darektar UNEP Ta Nuna Yabo Ga Matakan Kasar Sin Na Kiyaye Muhallin Halittu

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version