Maciji Da Bera Sun Zama Manya A Gwamnatin Buhari

El-Zaharadeen Umar, Katsina 08062212010

Duniya rawar ‘yan mata, na gaba ya koma baya inji masu iya magana, wannan karin magana ya yi dai dai da irin abubuwan da suke faruwa a wannan kasa da ake kira Nijeriya wajen canza abu daga yadda yake zuwa wani abu da ban musamman idan abun ya shafa al’umma kai tsaye.
Muna iya cewa Nijeriya ce kasa kwara daya da take da wayayyo kuma goggagun mutane da suka san yadda za su tafiyar da ‘yan kasa yadda suke so ba tare da sanin cewa kan mage ya waye ba, kuma Makaho bai san ana kallonsa ba sai ya ga bai da sanda.
Shi yasa yanzu idan wasu kasashen suka kalli Nijeriya ko ‘yan Nijeriya suka ce baku waye ba, baku da Ilimi, tsiya ta yi maku kanta, ba ku san abinda kuke ba, ba ku da shuwagabanni, har yanzu baku san inda ke yi maku ciwo ba, dabbobi sun fi ku kima da jamurta a kasarku, bana tunanin wani zai daga yatsa ya ce an yi ba dai dai ba.
Domin kuwa a yanzu hakan bayanan da suke yawo a kafafen sadarwa musamman na sociyal midiya a yanzu su ne, yadda aka samu wani gawurtaccen maciji ya yi wa naira miliyan 36 hadiyar kafino a ofishin hukumar jarabawar shiga jami’a (JAMB) wanda hakan irin sa ne na farko a tarihin wannan hukuma da kuma kasa baki daya.
Abin lura anan shi ne, matar dai ta yi wannan bayani ne, a matsayin iyakar gaskiyar ta a wajan ‘yan Nijeriya sai dai ana iya samun wasu bayanai kila idan za a zurfafa bincike domin kara jin wasu batutuwa masu dauka hanali da haushi da kuma ban dariya.
Hakkika duk wanda ya ji batun da farko dariya ya yi, amma daga baya saboda sanin hali, wai kare ya ci alli, sai kawai a basar saboda a Nijeriya ne abubuwan da ake da tabbacin ba za su faru ba sai su faru, wadanda ake da tabbacin za su faru sai kuma a ga akasin haka, domin haka Nijeriyar ta koma.
Abinda yasa na yi wa wannan rubutu na yau taken Maciji Bera sun zama manya a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, shi ne ko ba komi, ba a da da dai daga fita daga badakalar yadda bera ya hana shugaban kasa zuwa ofishinsa a cikin fadar gwamnatin tarayya ba nkwatsam sai ga wannna sabuwar al’amarar ta Maciji ya cinye naira miliyan 36.
Bayanan da za su biyo baya sune za su tabbatar da kasancewar wadannan dabbobi sun zama manya a cikin wannan gwamnati domin a tunani irin na dan adam ko mutun ne ya yi abinda wadannan dabbobin suka yi sai ya fuskancin fushin ‘yan Nijeriya balantana dabbobin da ba sa zaune a cikin mutane.
Lokacin da wannan lamari ya faru kowane dan Nijeriya ya yi fatan cewa ina ma za a ba su dama su yi fito-na-fito da wadannan beraye domin dai ko ba komi za su cutar da ‘yan kasa saboda hana shugaban kasa aiwatar da aikinsa yadda ya kamata.
To, amma wani batu da yake daure kan ‘yan Nijeriya shi ne, sun kasa gane wanda ya yi dogon bincike ya gano cewa duk abinda aka fadawa ‘yan Nijeriya za su amince su kuma yadda da shi ya zama daiadai ba tare da neman karain bayani ba saboda yadda ake kallonsu cikin bakin jahilci.
Kodayake wasu da dama sun nemi a yi masu bayani dalla-dalla (Interpretetion) akan sabbin kyankyasan berayen da suka gawurta sannan suka samu wurin zama a cikin fadar shugaban kasa, bayan haka kuma har sun sami damar hanashi shiga ofis domin gudanar da aikinsa a matsayinsa na shugaba mai cikakken iko.
Alal hakika ire-iren wadannan kalamai ko batutuwa sun taimaka wajen kara zubar da kimar Nijeriya da ake ganin ta rage a idon ‘yan kasa da kuma sauran kasashe musamman wadanda suke tsararrakinta ne, sannan ga su kuma ‘yan kasa ya zama abin kunya irinsa na farko a tarihin kasarsu.
Babu shakka akwai abubuwan da suke faruwa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari sun yi kama da yadda dabbobi ke rayuwa a cikin dokar da ji, inda ya zamana babu mai iko sai wanda ya fi karfi, babu mai shanawa sai masu mulki, babu mai cewa a’a sai wanda ya murje idonsa.
Idan ba haka ba, me yasa Malam Garba Shehu ya kware wajen tozarta Nijeriya da maganganu marasa amfana da kima a idon duniya? Me yasa duk wata wauta a wajansa ake jiran a ji fitowarta? me yasa yake ajiye abinda ake kira doka ya yi abinda ake kira san rai? Me yasa kullun yake mantawa da haduwa da ubangijinshi? Me yasa ya fifita duniyarsa akan lahirarsa?
Rashin kula da abubuwan da na zayyana wanda Garba Shehu ya dauka amatsayin aikin da ke gabansa wanda kuma yake a shirye wajen yin su kodayaushe ba zai taba bari ba, ‘yan Nijeriya su gane cewa Bera ba karamin abu bane a wannan gwamnatin da ake kallo kamar ta sahabai.
Bari mu dawo akan maganar macijin da ya yi wa naira na gogar naira har naira miliyan 35 hadiyar kafino kila ko ruwa bai hada da su ba, kai kasan wannan maciji ya cuci ‘yan Nijeriya da dama kuma bayanan da muke samu shi ne ba a nasarar damke macijin ba sai dai mai wannan maciji yana fuskantar bincike a halin da ake yanzu.
Wannan batu kamar yadda na fada tun da farko ya zo ma da wasu da mamaki wasu kuma tuni sun sa za ayi haka, tunda Nijeriya ce komi na iya faruwa amma dai wasu sun ce wannan lamari akwai rainin wayau sanfarin farko a cikinsa.
Ga dai wasu ra’ayoyin ‘yan Nijeriya dangane da wannan wulakanta kai, inda wasu ke cewa kun taba ganin maciji ya hadiye naira miliyan 36? Rahotanni sun ce an tara kudin ne daga sayar da katin da ake duba sakamakon jarrabawa.
Haka kuma masu amfani da shafukan zumunta a Nijeriya sun yi ta arashi da suka kan yadda wata ma’aikaciyar hukumar tsara jarrabawar shiga jami’a JAMB, ta ce maciji ya hadiye naira miliyan 36 na hukumar, reshen jihar Benue.
Ita dai Philomina Chieshe ta yi ikirarin cewa wani “hatsabibin maciji” ya shiga ofishin hukumar inda ya je wurin da ake ajiye kudi ya hadiye naira miliyan 36. Haka rahotanni sun ce an tara kudin ne daga sayar da katin da ake duba sakamakon jarrabawar ta JAMB.
Ya zuwa yanzu bayanan da ke fitowa sun tabbatar da cewa an dakatar da matar, sannan an kaddamar da bincike kan yadda “maciji ya hadiye kudin.” Hukumar EFCC, wadda ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, ta aike da sakon Twitter inda take cewa ba za ta yi rahama ga macijin da ke hadiye kudi ba.”
A Nijeriya dai an sha samun yanayi daban-daban da kudin gwamnati ke yin batan dabo, amma a iya cewa wannan ne karo na farko da aka taba zargin wata dabba da dauke kudi sai dai an taba zargin bera da hana shugaban kasa shiga ofis nya gudanar da aikinsa.
Idan muka yi karatun ta nutsu akan wadannan abubuwan da suka faru akwai darussa da daman gaske da yakamata kowane dan Nijeriya ya dauka ta yadda nan gaba komi zai faru za a san ta inda za a bullowa abin, amma idan aka rike hannu aka zuba ido to akwai abubuwan da za su faru masu yawan gaske.
Daga cikin abubuwan rainin wayau da wasa da hankali da za su biyo bayan wadanda suka gabata suna da yawa kuma za su fi so sa zuciyar ‘yan Nijeriya, kila nan gaba ace wani shaho ya dauki akwatin zabe mai dauke da kuri’a miliyan daya kuma maganar ta tafi a haka.
Kila nan gaba a ce motar shugaban kasa ta sha man fetur na miliyan 100 a ranar daya da dai sauran maganganu marar sa tsari. Kazalika wasu sun yi tunanin cewa hatta wadanda suka gama mulki a shekarun baya da wahala su yi abinda wadannan mutanen suke yi.
Gaskiyar maganar shi ne, dole hukumomin tsaro da kungiyoyi masu fafutukar yakin da cin hanci da rashawa su nuna jan ido akan irin wannan badakala irinta ta farko a tarihin duniya domin hana wasu damar nan gaba kara yin wata kashashaba.
Kuma idan har hukumomi da masu mulki za su rika amfani da karfin mulkinsu wajen raina hankalin ‘yan Nijeriya ta hanyar yin maganganun ‘yan matan amarya abubuwan da za su biyo baya nan gaba, ba masu kyau ba ne, kuma nan gaba sai an rasa wanda za a kalla a yi masa kwatankwacin irin wadannan maganganu.
A karshe muna jiran Garba Shehu da martani daga fadar shugaban kasa domin jin wani sabon al’amarin mai ban mamaki tunda anan bangaran ya fi kwarewa, tunda yanzu ayar tambaya tana nuna shi, in dai ka ji ya yi magana to dayan biyu sannan a jira, za a ji maganar ba dadi ba hikima cikinta balanta tausayawa.

Exit mobile version