Zaman da ‘yan majalisar dokokin Jihar Ondo suke yi ya watse babu shiri a ranar Alhamis, a sakamakon yanda macizai masu rai suka yi ta fadowa a cikin zauren majalisar a daidai lokacin da ‘yan majalisar suke cikin zaman su.
An ce hakanan kawai aka ga macizai suna ta fadowa daga saman Ceiling din zauren majalisar a ranar Laraba da kuma Alhamis.
A cewar wata majiyar, macijin da ya fado a cikin zauren majalisar a zaman majalisar na ranar Alhamis, kiris ya rage da a kan Kakakin Majalisar, Mista Bamidele Oloyeloogun, ya fada a daidai lokacin da yake jagorantar zaman majalisar.
Fadowar macijin ya sanya zaman majalisar ya watse ba tare da yin ko da addu’ar rufe zaman ba.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa, ya zuwa yanzun an dage duk wani zama na majalisar har sai an gano inda gizo ke sakar gami da sake fasalin majalisar baki-dayanta domin gudun sake aukuwan wannan lamarin mai ban tsoro da ya firgita Honorabuls din.