Daga Idris Umar,
Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaidi yadda bukin ya gudana.
Wannan makaranta dai tana anguwar Kwangila ne da ke karamar hukumar Sabon Gari, a jihar Kaduna. An gudanar da taron bakidaya ne a wani babban fili da ke anguwar ta Kwangila.
Jama’a ne daga ne daga bangarori daban daban suka sami halartar taron gami da Staten dalubai ciki har da Catalina da manyan ‘yan siyasa.
Bayan kammala komai ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin wasu dalubai game da samun kansu da suka yi a cikin masu sauka.
Awwal Iliyasu (Abba) dan shekara 25 ne yana cikin masu sauka a nasa bayanin cewa ya yi yana godiya ga Allah sannan yana godiya ga iyayensa bisa bashi goyon baya da suka yi, kuma ya godewa malamansa bisa yadda suka yi hakuri da shi game da bashi wannan ilimi na Al’kur’ani dan haka ya yi fatan alkairi ga duk wadanda suka bashi goyon baya. Ita ma Murjanatu Hashim tana daga cikin ‘ya ‘ya mata da suka sami damar saukar, a nata bangaren kira ta yi ga ‘ya ‘ya mata ‘yan uwanta da su kara kaimi a wajen karatun Al’kur’ani mai girma haka zai sa su sami dama a duniya da lahira ta yi godiya ga iyaye da malamai da suka bata wannan damar.
Malam Abdullahi Suleman Dan masanin Kwangila shine shugaban makarantar, shi kuwa kira ya yi ga iyaye da su kara kaimi wajen bayar da kudin makaranta tare da tura yara a kan lokaci. Kuma ya yi roko ga masu hannu da shuni da su kalli halin da makarantar ke ciki domin bayar da tasu gudummuwar dan samun cigaban ilimi a wannan yankin.
Alhaji Abdullahi Sale shine sarkin Kwangila shi kuwa yabo ya yi ga dalubai da su kansu malamai a wurin saukar. Na farko ya ja hankalin dalubai da su yi karatu domin Allah, kuma ya ja hankalin malamai da su koyi hakuri da kai zuciya nesa yayin koyar da dalubai. Karshe ne ya yi kira ga duk jama’ar da ke gurin da su kiyaye dokokin da gwannati ta sa domin kare lafiya, kuma ya yi fatan alheri ga duk wadanda suka bada gudummuwa musamman kungiyar masu kula da marayu bisa kokarin da suka yi a wurin. Binciken da jaridar Leadership Ayau ta yi shi ne wannan macadamia ta fara ne da dalubai 2 amma yanzu tana da dalubai 1257.
Kuma bincike ya abatar har yanzu wannan makaranta ba ta da muhalli na ta na kanta, duk karatu ana yinsa ne a zaurukan jama’a a matsayin aro. Bugu da kari bincike ya abatar akwai marayu masu yawa a makarantar kuma makarantar na bukatar kayan aiki na zamani wajen gudanar da karatu.
Binciken ya tabbatar da cewa akalla mata 29 ne suka sami shaida maza 10. An yi taro lafiya an tashi lafiya.