Madinatul Ahbab Ta Yi Walimar Haddar Alkur’ani Na Dalibai 24  A Wudil

Madinatul Ahbab

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Makarantar Madinatul Ahbab reshen Karamar Hukumar Wudil ta gudanar da bikin saukar karatun Dalibai 18 Kuma guda shida  da Suka Samu haddace littafin Allah.

Da yake gabatar da jawabin maraba Shugaban rukunin Makarantun Madinatul Ahbab na kasa, Sheikh Faralu Dan Almajiri Wanda ya samu wakilcin khalifansa Sheikh Tijjani Sheikh Dan Almajiri, ya bayyana farin cikinsa da wannan rana, inda ya godewa shugaban majalisar mahaddata alkur’ani na kasa bisa samun sukunin halartar wannan taro. Daganan sai ya jinjinawa kokarin malaman da ke jagorancin wadannan makarantu, wanda ko shakka babu sun canci Jinjina.

Da yake gabatar da jawabinsa Shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani Na Jihar Kano Goni Sunusi Abubukar ya bukaci dalibai su fahimci cewa yanzu ya kamata su kara Jajircewa wajen riko da littafin Allah. Daganan sai ya bukaci duk inda ake gudanar da karatukan Alkur’ani lallai a ci gaba yin addu’ar fatan Dorewar zaman lafiya a Jihar Kano da kasa baki daya.

Shima Sarkin Malaman Wudil Gwani Malam Musa Yaya Wudil ya tabbatar da aniyar Malamai aduk Inda suke na dukufa da yin addu’o’in dorawar zaman lafiya a kasarnan, musamman ganin halin da ake ciki na tashin tsaro da matsin tattalin arziki. Saboda haka sai ya taya wadannan dalibai murnar samun wannan baiwa da yace ba kowa Allah ke baiwa irinta ba.

Shima anasa jawabin gudan cikin masu  jagorancin wadannan Makarantu na Madinatul Ahbab, wanda kuma shi me sakataren tsare tsare na majalisar mahaddata na Jihar Kano sannan kuma daraktan ayyuka na musamman a matakin kasa Gwani Laminu Mahmud Salga ya bayyana farin cikinsa da ganin yadda ake kara samun yaran da Allah ke horewa haddar Alkur’ani, yace wannnan abin farin ciki ne kwarai da gaske.

Gwani Aliyu  Salihu Turaki Shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani Na Kasa, kuma babban limamin babban  Juma’a na Alhassan Dantata Shi ne ya biyawa daliban allunansu, ya yinda Sarkin Malaman Wudil, Gwani Malam Musa Yaya Wudil ya biyawa sauran daliban allunansu. Gwanaye da Gangarayen Alkur’ani ne suka duba allunan daliban a yayin saukar karatun

Taron saukar ya samu halartar shugabani Mahaddata Alkur’ani Na Kasa Gwani Aliyu Salihu Turaki, Goni Sunusi Abubukar, Gangaram Alaramma Malam Muhammad Auwal Isa Gaya, Gwani Sabo Mukhtar Mai rigar Fata, Sarkin Malam Wudil, Gwani Malam Musa Yaya, Gwani Hammadu M. Uzairu da sauran manyan baki daga wuraren daban-daban me Suka shaida wannan sauka.

 

 

Exit mobile version