Daga Abba Ibrahim Wada
Real Madrid za ta ziyarci Fuenlabrada domin karawa da ita a gasar Copa del Rey a yau Alhamis.
Madrid wacce ke ta uku a kan teburin La Liga za ta buga wasan kungiyoyi 32 da suke buga gasar.
Wasu wasannin da za a yi a ranar ta Alhamis Lleida Esportiu da Real Sociedad, Deportiɓo La Coruna da Las Palmas, Girona da Leɓante da karawa tsakanin CD Tenerife da Espanyol.