Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ILIMI

Madubin Imani

by Tayo Adelaja
October 1, 2017
in ILIMI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

 

Sunusi Shehu Daneji             +2348135260786 sshehudaneji52@gmail.com

samndaads

Kamar yadda a ka san cewa Dare da Wuni su na samuwa ne a sakamakon juyin da kwallon duniya ya ke yi, to haka dai a cikin hikima da bajintar iya tsari na mahalicci Allah, ya tsara duniyar ta na tafiya don kewaya Rana wanda da hakan ne kuma a ke samun tsawon shekara.

Har wa yau kuma tasgadawar da duniyar ta yi da ita ne a ke samun sauyin lokaci hudu da a kan samu a tsawon shekara. Wato lokutan Hunturu da Bazara, sannan da lokutan Damina da Kaka.

A zahiri wannan hajijiya ta zarci gudun da duka wani jirgin sama ke yi. Harwayau, kamar yadda aka fada a baya, Duniya na yin tafiyar mil 60,000 a dukkan awa daya, don kewaya Rana, kimanin kilomit 100,000, wato daidai da tafiyar mil 1,000 a duka minti daya kwatankwacin gudun da ya zarci gudun harsashin bindiga sau 100. Wato a duka sakan daya na agogon hannunmu Duniyar nan tamu ta na tafiyar mil 19.

Duniya na kammala yin juyi guda a tsawon awa 24, wato ta na juyawa juyi guda a duka kwana daya (awa 24), sannan ta na tafiya ta kewaya Rana kewaye daya a tsawon kwanaki 365.

Saboda kasancewar duniya wani mulmulallan abu, can samanta, kurewar arewaci da kudancin dwallon duniyar, ya kan sami bambanci na miki darin juyi saboda kusanci.

 

Maganadison Duniya

Hakika wannan duniya tamu ta na da wata kuwwa me karfin gaske ta maganadiso da Allah mahalicci ya tsara ta da shi. A zahiri wannan maganadiso an tsara shi a yanayin da ya kan samar da wata kariya ta musamman ne ga kwallon wannan Duniya tamu. Don haka wannan maganadiso, musamman ya na da wata kuwwa me tasiri a kusurwarsa ta Arewacin duniya da kusurwarsa ta Kudancin duniya, kamar yadda aka san mayen karfe ya ke da su.

Wannan maganadison duniya, ya na samun tasirin kara karfinsa ne daga irin motsin da doron duniya ya ke yi, saboda irin tarin sinadaran da ke can tsakar duniya su ke. Wato wannan maganadiso ya na canza kan saya kara karfi daga motsin da kwallon duniya ke yi, kamar yadda batirin mota ko babur ke caza kansa yayin da abin hawan ya ke aiki.

Duniyar nan tamu ta Ardhu ce kadai a duniyoyi ’yan Tawagar Rana ke da wannan kariyar, kuma ga nazari na masu kimiyar Sararin Samaniya, idan ba don wannan kariya da Allah ya tsara kwallon Duniya da ita ba, da raina kowanne irin halitta ba zai iya rayuwa ba, haka nan kuma da duka yanayin da ke sararin saman Duniya ya kekashe, sannan kuma da duka teku da tafkunan ruwa sun kafe.

Har ya zuwa yau, ga dukkan matsanantan bincike da Dan-adam ya ke yi, Duniyar nan tamu kadai ce Duniyar da Allah ya sanya Rai ya ke raye a ciki. Wannan salon Rai ya hada Rayuka na sauran abubuwan halittu iri daban-daban, kama tun daga irin su ran gansa-kuka da irin rai na su matsattsaku da mu mutane da kananan kwari, kama har ya zuwa ga Ran manyan dabbobi na dawa da na ruwa da ma wadansu da ba a iya ganowa ba.

Masu kimiyya rbinciken Samaniya sun tabbatar da Duniyar nan ce kadai ke da rayuka rayayyu, haka nan kuma bisa ga binciken tsirrai da halittu, an tabbatar da cewa akwai Rayuka na halittu daban-daban da su ka wanzu su ka rayu a doron kasa kwatankwacin salon Rai miliyan biyar zuwa salon Rai miliyan 100. Amma a halin yanzu a na tsammanin za a sami salon Rai miliyan 2 ne da a ka iya fahimtar su na rayuwa a duniyar tamu.

Sai dai har kullum masu ilimin kimiyar Samaniya su na ta bincike a wasu gurare da ke Samaniya, don gano inda za a sami Rai a kowacce irin siga, amma dai har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba.

Bisa ga wannan bincike an sanya bincike a kan wani wata na duniyar Saturn mai suna TITAN da wani wata na duniyar Jupiter mai suna EUROPA, wadanda dukkansu wurare ne da a ka fahimci su na da yanayi, kuma yanayi na ke tsammanin za su iya rayar da Rai.

SendShareTweetShare
Previous Post

A Na Kashe Naira Biliyan Takwas  Wajen Shigo Da Shinkafa

Next Post

Farfaganda Ko Kama-karya: Da Me Masari Zai Nemi Tazarce A Jihar Katsina?                           

RelatedPosts

Me Yasa Ake Dakile Ilimin Mata A Arewa (1)?

by Sulaiman Ibrahim
6 months ago
0

SHIMFIDA. Lokacin da aka sace daliban makarantar Chibok a jihar...

Hana Barace-barace Shi Ne Mafi Alheri Ga Al’umma – Pantami

Zuwa Ga Shugaba Buhari!

by Daurawa Daurawa
9 months ago
0

Barka da shan ruwa, da kuma fatar Allah ya amshi...

Mafita Kan Yadda Aka Yi Watsi Da Ilimi A Arewa

Mafita Kan Yadda Aka Yi Watsi Da Ilimi A Arewa

by Sulaiman Ibrahim
9 months ago
0

Ilimi haske ne da shiriya, kamar yadda jahilci duhu ne...

Next Post

Farfaganda Ko Kama-karya: Da Me Masari Zai Nemi Tazarce A Jihar Katsina?                           

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version