Madubin Imani

Sunusi Shehu Daneji +2348135260786 sshehudaneji52@gmail.com

RANA da duka duniyoyi tara tare da duk duwatsun da Allah ya halitta da ke dawafi suna kewaya Ranar su ne TAWAGAR RANA.

Rana da a kullum ta kan fito ta haska mu ga haske, ta kasance Tauraruwa daya da Allah ya tsara take gaba wajen gudanar da lamuran tawagarta.

Kashi 99 na makamashin dake ga dukkan Tawagar Rana yana ga ita Ranar ne.

A wannan Tawaga ta Rana, akwai duniyoyi guda 9 da watanni kimanin guda 90 da duwatsu sama da biliyan 1000.

Bisa ga nazarin kimiya, Allah mahalicci ya samar da duka wadannan abubuwa tun kimanin shekaru biliyan 4 da miliyan 600 da suka gabata daga sinadarai daban daban na cinkoson hayaki da iska masu tarin yawa.

Tsarin samuwa na wadannan duniyoyi na Tawagar Rana, ya rabu rabo biyu. Rabo na farko su ne duniyoyi hudu makusanta da Rana, kamar DUNIYAR MAKYURE da DUNIYAR ƁENUS da DUNIYAR ARDHU da DUNIYAR MAS.

Duka wadannan duniyoyi hudun, duniyoyi ne na tsandaurin kasa da dutse. Kuma a duka wadannan duniyoyi hudu makusanta da Rana, duniyarmu ta Ardhu ne kadai Allah ya sanya ta ke da wata guda daya rak.

Acikin duniyoyi hudu makusanta Rana, duniyar MAKYURE ce ta farko, sannan sai duniyar BENUS. Daga nan sai duniyarmu ta ARDHU. Ta hudu a duniyoyi hudu makusanta Rana, ita ce duniyar MAS. Daga nan sai ragowar duniyoyi biyar na Tawagar Rana da suke nesa da kwallon Rana. Akwai duniyar JUFITA da duniyar SATAN (me zobe) da duniyar URINAS da duniyar NEFTUN.

Wadannan duniyoyi hudun kuma duka curin manya manyan gajimarai ne na iska da kura da Allah me hikima ya tsara suke a mulmule a jikin dan mulmulan kasa da ke can tsakiyar duniyoyin. Duka wadannan duniyoyi suna da watanni, wasunsu suna da zobe na kura da ‘yan kananan duwatsu da suka yi musu kawanya da take kewaya su.

Duniyar JUFITA ita ce duniya ta biyar, kuma duniya mafi girma a duka Tawagar Rana. Duniyar SATAN, ita ce duniya ta shida, kuma tana da zobe na kura mai girma da Allah mahalicci ya tsara mata yana kewaya ta. Duniyar URINAS, ita ce duniya ta bakwai, sannan sai duniyar NEFTUN, duniya ta takwas.

Duniya ta tara kuma ta karshe a cikin wannan Tawaga ta Rana, ita ce duniyar FULUTO, wadda a halin yanzu masu kimiyar Samaniya suka ce ba duniya b ace saboda dabi’unta sun bambanta da dabi’un suffa ta duniyoyi.

Ita wannan duniya ta Fulutu, ‘yar karama ce wadda curin kasa da dutse ce, amma tana da ‘yar dusar kankara da ta dan baibaye jikinta.

A wannan Tawaga ta Rana, akwai wasu tarin duwatsu rukuni biyu da Allah me iko ya tsara suke kewaya Rana a nasu muhallin kamar yadda duniyoyi ‘yan Tawagar Ranar suke kewaya Ranar. Muhalin kewaye na farko na wadannan duwatsu, shi ne ya raba duniyoyi hudu ‘yan kusa da Rana da duniyoyi biyar na nesa da Rana. Muhalli na biyu na wadannan duwatsu shi ne na can bayan duniya ta karshe, kafin karshen da’ira ta gabar Tawagar Rana.

A wannan da’irar duwatsu ta karshe ne Allah me iko ya sanya duwatsun Taurari Me Wutsiya da a kan gani lokaci lokaci. Allah a cikin iyawarsa, ya tsara duka duniyoyin nan suna dawafi daga kan falakin da kowacce duniya ke kai tana mazari tana kuma nunkaya.

Falakin kowacce duniya ba wata turba ko shata me shimfidar titi ba ce da ke da wata alama, face dai iko ne da iyawa na mahalicci Allah da ya tsara kuma yake shiryar da duniyoyin ga bin hanyoyin da za su kai ga ida nufi. Duniyoyin duka suna tafiya ne a sarari cikin kudurar mahalicci Allah cikin tsari. Don haka Falaki suna ne kawai na tafarkin da ake aiyanawa duniyoyin suna tafiya a kai.

Akwai babbar hikima wajen yadda Allah mahalicci ya tsara tsarin wannan Tawaga ta Rana, domin dai cikin iyawarsa ya sanya Rana wadda ke da karfin Magana dison me girma da zai iya tasiri ga duka abubuwan da suke tawagar ce a tsakiyar Tawagar.

Karfin Magana dison Ranar na iya jan sauran duniyoyi tara da duka halittun duwatsu da ke Tawagar a sami daidaiton da zai iya daidaita Tawagar gabadaya daidaito na komai da yake gudana.

 

MOTSI

Hakika yana daga hikima ta mahalicci Allah ta yadda ya sanya daidaito a gudanarwar Tawagar Rana.

Dukkan duniyoyi da watanninsu tare da duka duwatsun da ke tawagar suna kan tsari bai daya, kuma cikin daidaito. Dukkan duniyoyi tara suna kewaye Rana kuma suna katantanwa daga Hagu zuwa Dama. Dukkan manyan watannin duniyoyin su ma su na kewaya Duniyoyin suna katantanwa daga Hagu zuwa Dama. Ita kanta Rana tana yin katantanwa daga Hagu zuwa Dama, kuma tana tafiya don kewaya tsakiyar Birnin taurarin da take.

 

TAZARA

Duniyar MAKYURE ita ce duniya mafi kusa da Rana, tana da tazara ta mil miliyan 36 daga Rana. Kwana 88 ne shekara guda a kan duniyar MAKYURE, kuma kwana 59 ne kwana guda na duniyarmu. Sararin kan duniyar Makyure sarari ne me kamfa da kwazazzabo da tsaunuka. Wannan Duniya ta Makyure duniya tsananin zafi, kuma iskarta tsikakkiya ce. Yanayin zafi a sararin duniyar Makyure ya kan kai digiri 450 salshiyos a lokacin wayewar gari, yayin da ya kan sauka zuwa 170 idan dare ya yi.

 

Exit mobile version