MADUBIN IMANI

Sunusi Shehu Daneji +2348135260786

sshehudaneji52@gmail.com

Duniyoyi

Duniyar ƁENUS wato zara matar wata, uta ce duniya ta biyu daga Rana. Tana da tazarar mil miliyan 67 daga Rana, kuma kwana 225 na duniyarmu ne shekara guda a kanta. Yayin da kwana 243 ne kwana guda. Duniyar Ɓenus na da yanayi mai yawan gajimarai da iska tsikakkiya. Yanayin zafinta yana kaiwa digiri 470 salshiyos.

Duniyarmu ta ARDHU ita ce duniya ta uku daga Rana, tana da tazara ta mil miliyan 93 daga Rana. Kuma tana da yanayi madaidaici da yak an bar ruwa ya dauwama sigar uku ta iska da ruwa da a kankara. Har wa yau Allah ya sanya mata yanayi wanda yake baiwa mutum kariya daga manyan abubuwa masu cutarwa. Ga missali tana da yanayi da ya kan kone fandararrun duwatsun da kan  keto duniya daga Samaniya. Sannan kuma yanayin kan duniyar nan tamu ya kan iya kare tsananin huci Rana da na Samaniya da ka iya cutar da rai. Duniyar tamu ta Ardhu na da girma wanda ya kai da’ira ta tafiyar mil 25,000 na kewaye. Kuma Duniyar tamu ce kadai take da wata guda daya.

Duniyarmu ta Ardhu na da tazara ta tafiyar mil miliyan 93 daga Rana, kuma tana kewaya Rana kewaye guda a tsawon kwanaki 365. Tana tafiyar mil 19 a dukkan sakan daya.

Duniyar MARIS ita ce duniya ta hudu daga Rana, kuma tana da tazarar mil miliyan 141 daga Rana.

Kwana 687 ne shekara guda a duniyar Maris. Yanayin zafi a kanta ya ka digiri 35 na salshiyos, da daddare kuma yakan suka zuwa sanyi a awon digiri na -170. Wannan duniya ta MARIS tana da ‘yan watanni kanana guda biyu. Duniyar MARIS duniya ce me tarin hanyoyin masu kwazazzabai.

 

JUPITER

Itace duniya ta biyar, kuma itace dauniyar da ta fi kowacce duniya girma a duka duniyoyi da suke Tawagar Rana.

Akalla za a iya cusa duniyarmu ta Ardhu guda 1,500 a cikinta.

Shekara guda a kan Duniyar Jupiter su ne shekaru 11 da wata 8 na duniyarmu ta Ardhu.

Tana da tazara ta mil miliyan 484 daga Rana.

Kwana guda a kanta awoyi 10 ne kawai.

Tana da watatnni 63, hudu ne manya sosai.

 

SATURN

Duniya ta shida Rana itace duniyar Saturn (Duniya me zobe).

Wannan duniya itace ta biyu a girma a duka Tawagar Rana. Tana da tazara ta mil miliyan 887 daga Rana, kuma shekara guda a kanta, su ne shekaru 30 na duniyarmu ta Ardhu.

Awoyi 10 ne kwana guda a kanta.

Zoben da ya kewaye wannan duniya ta Saturn zobe ne na kura me tarin duwatsu a cikin yanayi na guguwa me kadawa da sura irin na kawanya.

Wannan duniya ta Saturn na da watanni 21 na sama da ke gani.

 

URANUS

Duniyar Uranus ce duniya ta bakwai daga Rana. Tana da tazara ta mil miliyan 1,784 gada Rana, kuma shekara guda a kanta yana matsayin shekaru 84 a duniyarmu ta Ardhu. Awoyi 17 ne kwana guda a kanta.

Wannan duniya ta Uranus ce kadai Allah ya tsara mata take juyi a kwance, maimakon a tsaye kamar ‘yan uwanta duniyoyi.

Tana da watanni 15 na sama da ke gani.

 

NEPTUNE

Wannan duniya ta Neptune, ita ce duniya ta 8 daga Rana. Tana da tazara ta mil miliyan 2,795 daga Rana.

Shekara guda a kanta tana daidai da shekaru 165 na duniyarmu, kuma awoyi 17 ne kwana guda a kanta.

Tana da watanni 8 na sama da ke gani.

 

PLUTO

Duniyar PLUTO ce duniya ta tara, kuma mafi kankanta a duniyoyi ‘yan tawagar Rana.

A halin yanzu ma, masu kimiyar sararin Samaniya sun cire wannan duniya daga jerin duniyar da ke cikin wadanda a ke dauka daya daga ‘yan tawagar Rana.

Wannan ‘yar duniya ta PLUTO na da tazara ta mil milyan 3,667 daga Rana, kuma shekaru 248 na duniyarmu ne shekara guda a kanta. Kwana shida da ‘yan awanni ne kwana guda a kanta.

 

ASTEROID

Duwatsun Asteroid wadansu halittu ne da Allah cikin ikonsa ya tsara su kewa Rana daga Hagu zuwa Dama kamar yadda a tsara duniyoyi suke yi a tawagar Rana.

Wadannan duwatsu kanana ne da mafi girmansu bai fi girman tafiyar mil 200 ba, kuma dukkanin wadannan duwatsu ana samun su ne a iya bigiren da Allah mahalicci ya sanya su na tsakanin duniyoyi ba. Lokaci lokaci ana samun fandararru daga cikinsu su ketara da nufin fadawa wasu guraren da Allah ya yi nufin za su fada ba.

Akwai wasu daga cikin fitattun duwatsun Asteroid da aka shaida aka nazarin lamuran kai kawonsu.

Akwai dutsen Asteroid PALLAS wanda ya da girman tafiyar mil 325.

Akwai dutsen Asteroid ƁESTA wanda ya da girman tafiyar mil 310.

Akwai dutsen Asteroid JUNO wanda ya da girman tafiyar mil 150.

Mafi girma daga duwatsun Asteroid shi ne dutsen Asteroid CERES wanda girmansa ya kai tafiyar mil 575.

 

Exit mobile version