Connect with us

KASASHEN WAJE

Maduro Zai Nemi Tallafin Dala Miliyan 500 Daga MDD

Published

on

Shugaban Benezuela Nicolas Maduro, ya ce zai nemi majalisar dinkin duniya ta bashi tallafin dala miliyan 500, domin taimakawa gwamnatinsa wajen maido da dubban ‘yan kasar da suka tsrrewa munin halin da durkushewar tattalin arzikin kasar.

Shekaru hudu kenan bayan da tattalin arzikin kasar Benezuela ya fada cikin mawuyacin hali , inda a halin masana suka yi hasashen cewa, hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasar ka iya kai wa kashi miliyan daya bisa dari.

Wani rahoton baya bayan nan da majalisar dinkin duniya ta fitar, ya nuna cewa ‘yan Benezuela miliyan 2 da dubu 300 ne suke rayuwa a wajen kasar, kuma miliyan daya da dubu 600 daga ciki, sun tsere daga kasar ne tun daga shekarar 2015.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: